Ruɗani ya biyo bayan bayyanar kwafen hukuncin Klkotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan Jihar Edo a intanet, kwana guda kafin kotun ta yanke hukunci a hukumance. Kotun mai mutum uku, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Wilfred Kpochi, ta bayyana cewa za a yanke hukunci a ranar Laraba, 2 ga Afrilu, 2025. Sai dai kafin hakan, an ga wasu takardu da ke nuna hukuncin da kotun za ta yanke, wanda ya jawo ce-ce-kuce a tsakanin jama’a da ‘yan siyasa. Wannan al’amari ya tayar da cece-kuce a Edo, musamman tsakanin magoya bayan jam’iyyun da suka tsaya takara.
A cewar kwafen hukuncin da suka bayyana, akwai rabuwar ra’ayi tsakanin alƙalan kotun. Shugaban kotun, Mai Shari’a Kpochi, da wani alƙalin, mai shari’a A. B. Yusuf, sun yi watsi da ƙarar da jam’iyyar PDP da ɗan takararta, Asuerinme Ighodalo, suka shigar. Sun ce, ko da yake an samu matsaloli a zaɓen, ba su isa su canja sakamakon ba. A cewarsu, shaidu sun nuna cewa akwai kura-kurai kamar rashin rijistar wasu kayayyakin zaɓe da kuma ƙidaya ƙuri’u ba daidai ba, amma hakan bai isa ya shafi sakamakon ƙarshe ba.
Sai dai alƙali na uku, Mai Shari’a A. A. Adewole, ya bayyana akasin haka a hukuncinsa. Ya ce zaɓen bai bi ƙa’idojin dokar zaɓe yadda ya kamata ba, kuma akwai hujjojin da suka nuna cewa jam’iyyar PDP ce ta lashe zaɓen idan aka gyara kura-kuran da aka samu. Bisa haka, ya umurci hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) da ta soke shaidar lashe zaɓe da ta bai wa Gwamna Okpebholo, tare da ba Ighodalo sabon satifiket na nasara. Wannan hukunci na mai rinjaye ya sha bamban da na sauran alkalan kotun biyu, wanda hakan ya ƙara tayar da jijiyoyin wuya.
Bayyanar wannan hukunci a intanet kafin yanke hukunci a hukumance ya haifar da tambayoyi da shakku kan tsaron bayanai da ingancin aikin kotu. Wasu na zargin cewa an samu fitar bayanai daga cikin kotun, yayin da wasu ke ganin hakan wata dabara ce ta tasiri kan sakamakon ƙarshe. Yanzu haka, al’ummar Edo da ‘yan siyasa na dakon yanke hukunci daga kotu a hukumance, domin tabbatar da sahihancin sakamakon da za a fitar a ranar da aka sanya.
