
Daga BELLO A. BABAJI
Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta Kogi ta Tsakiya, ta sauka a mazaɓarta da ke Jihar Kogi a Arewacin Nijeriya.
Hakan na zuwa ne duk yunƙurin gwamantin jihar da rundunar ƴan sanda na hana zuwan sanatar.
A baya ne dai rundunar ƴan sandan jihar ta fitar da sanarwar barazanar tsaro, inda ta yi kira ga dakatacciyar sanatar da ta janye batun gangamin da aka shirya da sunanta.

