Haramta gangami ba zai hana ni zuwa gida hutun sallah ba – Natasha ga Gwamnatin Kogi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Talata ne Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da ke wakiltar mazaɓar Kogi ta Tsakiya ta bayyana cewa, ba za ta janye batun zuwanta gida hutun Sallah ba.

Ta yi kira ga magoya bayanta da su yi watsi da jita-jitar da ke yawo na cewa ta soke zuwa hutun Sallah.

Ta bayyana hakan ne ta hannun tawagar watsa labaranta a wata sanarwa.

Hakan na zuwa ne jim-kaɗan bayan Gwamantin jihar ta fitar sanarwar haramta yin gangami da wasu tarurruka bisa zargin barazanar tsaro.

Haka kuma ta dakatar da yin ayyuka kamun kifi (su) da makamantansa sakamakon rasa rayukan mutane biyu a Ƙaramar Hukumar Kogi ta Gabas.

Duk da haka, tawagar labaran ta ce, za a gudanar da taron zuwan sanatar, inda suke cigaba da shirye-shirye, ta na mai gayyatar ilahirin magoya bayanta da sauran al’umma zuwa wajen taron.

By Babaji