Daga USMAN KAROFI
Wasu matasa a yankin Iware, ƙaramar hukumar Ardo-Kola, Jihar Taraba, sun yi barazanar ƙona ofishin hukumar tsaro ta NSCDC bayan mutuwar wani mazaunin yankin mai suna Yunusa Kaka, wanda ake zargin jami’an hukumar sun azabtar har lahira.
Rahotanni sun bayyana cewa matsalar ta fara ne bayan kama wani matashi mai suna Biliaminu Adamu da ake zargi da satar wayoyi guda biyu da fakitin taba sigari. A lokacin da yake tsare, ya ce ya ba Yunusa Kaka wayoyin, amma Kaka ya musanta. Sai dai jami’an tsaro sun ci gaba da azabtar da shi don ya amsa laifin, wanda hakan ya janyo mutuwarsa.
Bayan labarin mutuwar Kaka ya bazu, matasa da dama sun yi ƙoƙarin kai hari ga ofishin NSCDC, amma jami’an tsaro sun hana afkuwar hakan. Duk da haka, hukumomi sun ce ana bincike kan lamarin don gano gaskiyar al’amarin.
