
Daga BELLO A. BABAJI
Ƙungiyar Masu Sharhi kan Harkokin Tsaro ƙarƙashin jagorancin Daraktan Tsaro a Shirin ‘Security of the Salute of Nigeria Initiative’, Kwamared Salihu Ɗantata Mahmud, ta yi kira ga Sufeton Janar na rundunar ƴan sanda, Kayode Egbetokun, da ya gudanar da bincike na sirri akan Hadiza Baffa, wacce ta zargi tsohon Ministan Ayyuka na Musamman, Tanimu Turaki (SAN) da cin zarafin.
Ɗantata ya nemi a yi binciken ne don tabbatar da gaskiya ko akasin hakan game da kalaman nata akan Turaki.
Ya ce, akwai da dama daga cikin waɗanda ta yi wa irin zargin da ke cikin kundin cibiyar manyan laifuka sun shirya kare kawunansu bisa halin nata da ke tattare da alamomin tambaya.
Ya kuma ce, da dama daga cikin makusantanta da ya gana da su sun shaida masa cewa tana da munanan halaye, don haka ne ya nemi ƴan sanda su shiga lamarin tare da haƙo haƙiƙanin gaskiyar al’amarin.
Kazalika, ya ce akwai buƙatar ƴan sanda su ziyarci jami’ar da ta baro inda ake zargin ba ta kammala ba, lamarin da ya sa ake mamakin yadda ta samu wasu bayanan, inda ya alaƙanta hakan da ƴan sandan Abuja, waɗanda su ma ya nemi a yi bincike akan su.
Ɗantata ya kuma ce, tsohon ministan ya na da kyakkyawan tarihi a harkar shari’a, siyasa da sauran nagartattun halaye, don haka ya ce wajibi ne a gare su su kare mutuncin masu mutunci.
