
Daga BELLO A. BABAJI
Shugaba Bola Tinubu ya bayyana alhini game da mummunan al’amarin da ya faru a wajen shaƙatawa na yara a Ibadan, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama tare da raunata wasu masu yawa.
Tinubu ya umarci hukumomin dake da alhakin binciken da su binciki musabbabin faruwar lamarin, kamar yadda Kakakinsa, Bayo Onanuga ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.
Shugaban ƙasar ya ce yana da muhimmanci a gano sakaci ne ya haifar da hakan ko kuma ganganci, ya na mai nuna muhimmancin tabbatar da adalci.
Ya kuma nemi Gwamnatin Jihar Oyo da ta ɗauki matakan kariya daga sake faruwa irin haka a nan gaba.
Cikin matakan akwai yin nazari game da shagulgula da wuraren gudanar da su da kuma ƙara inganta harkokin kariya ga al’umma.
Ya yi kira ga masu shirya taruka da su fifita bada kariya ga mahalarta musamman yara ƙanana.
Sannan, Shugaba Tinubu ya miƙa ta’aziyyarsa ga gwamnatin Oyo da iyalan waɗanda suka rasa rayukansu da jajenta wa waɗanda suka samu raunuka.
