Filin da aka ƙwace a Abuja ba na Buhari ba ne – Garba Shehu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Garba Shehu, Kakakin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi tsokaci game da ƙwace fili da aka yi a Abuja wanda aka ce na tsohon shugaban ƙasar ne.

Rahotonni sun bayyana yadda Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ƙwace takardun wasu filaye da adadinsu ya kai guda 762 a yankin Maitama dake babban birnin bisa rashin cike ƙa’idodi.

Waɗanda lamarin ƙwace takardun na ‘CofO’ ya shafa sun haɗa da na Gidauniyar tsohon shugaban ƙasa Buhari; tsohon Alƙalin Alƙalai, Walter Onnoghen; Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas; Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume da matarsa Regina; Gwamnan Kaduna, Uba Sani da sauransu.

Saidai a wata sanarwa da Shehu ya fitar a ranar Alhamis, ya ce Buhari ba shi ne asalin mai filin da aka ce an ƙwace ba, wanda aka sanya wa suna ‘Muhammadu Buhari Foundation’.

Ya ce tsohon shugaban ƙasar bai amince da rabon fili ba a lokacin da ya ke mulki don haka wanda aka ƙwace ba nasa bane.

Ya ƙara da cewa, a lokacin da ma’aikatansa suka kai masa takardar rabon filin, Buhari bai amince da ita ba, hasali cewa ya yi yana da fili a Abuja saboda haka a bai wa wanda bai da shi.

By Babaji