
Daga BELLO A. BABAJI
Olumuyiwa Adejobi, Kakakin rundunar ƴan sanda ya ce cin zarafi da ake yi wa waɗansu a kafar sadarwa babban laifi ne a ƙarƙashin dokar ƙasa.
A cikin wani rubutu da ya wallafa a shafin X, Adejobi ya bayyana irin aikin a matsayin cin zarafi ta yanar gizo wanda ba za a amince da shi a matsayin bayyana ra’ayi ba.
Ya ce cin zarafi a kafar sadarwa bai cikin ƴancin Ɗan-adam da dokar ƙasa ta sahale wa al’umma, saidai abu ne da ke zama aibu ga wanda aka yi wa.
Don haka ne ya yi kira ga ɗaukacin al’umma da su ƙaurace wa aikata laifin, ya na mai cewa duk wanda aka samu da hannu a cikin hakan, zai fuskanci hukuncin da doka ta tanadar.
