Tinubu ya yi jimamin rasuwar Babban Sakataren Majalisar Ƙolin Shari’a, Nafi’u Baba-Ahmed

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya bayyana jimaminsa bisa rasuwarsa Babban Sakataren Majalisar Ƙolin Shari’a a Nijeriya (SCSN), Malam Nafi’u Baba-Ahmed.

Malam Baba-Ahmed, wanda jami’in gudanarwa kuma jagoran addini da ake mutuntawa, ya rasu ne a safiyar ranar Talata bayan tsawon lokaci yana hidimta wa Musulunci da Nijeriya. Shugaba Tinubu ya bayyana marigayin a matsayin jagora mai tasiri da ya gudanar da harkokin SCSN bisa hikima, hangen nesa da ƙoƙarin samar da haɗin kai, adalci da zaman lafiya acikin al’umma.

Tinubu ya tunatar da alaƙarsa ta tsawon lokaci da shi musamman a lokacin shirye-shiryen zaɓen 2011 da kuma shekarun da suka biyo baya musamman wajen shawarwarin marigayin da goyon bayansa ga yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Haka kuma, Tinubu ya yaba wa marigayi Baba-Ahmed kan rawar da ya taka wajen ɗaga muryar majalisar akan muhimman al’amuran ƙasa, ƙarfafa kyakkyawar fahimta da kira ga kiyaye kyawawan ɗabi’u da adalci acikin al’umma. Kazalika, Tinubu ya jajenta wa Shugaban Majalisar Ƙolin, mambobinta, iyalan marigayin, gwamnati da al’ummar Jihar Kaduna da kuma ɗaukacin al’ummar Musulmin Nijeriya bisa babban rashin.

A ƙarshe, ya yi masa addu’ar Allah ya yafe masa kurakuransa ya kuma sanya shi a Aljannar Firdausi da bai wa makusanta haƙurin juriyan rashin sa, kamar yadda aka bayyana a wata sanarwa da Kakakin Shugaban Ƙasa Bayo Onanuga ya fitar mai ɗauke da kwanan wata 6 a Oktoba, 2026.

By Babaji

Leave a Reply