Mataimakin kwamandan Hisbah na Katsina ya yi murabus

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Mataimakin babban kwamandan hukumar hisbah ta Jihar Katsina mai kula da ayyuka, Muhammad Shitu Maslaha, ya yi murabus daga muƙaminsa.

Maslaha ya bayyana hakan ne a cikin wasiƙar murabus da ya sanya wa hannu inda ya ce zai fara aiki nan take.

Ya gode wa babban kwamandan Hisbah, shugabannin hukumar, mahukunta da sauran ma’aikatan hukumar bisa goyon baya da haɗin kan da suka ba shi a lokacin da yake aiki.

Sai dai, bai bayyana dalilin da ya sa ya ajiye muƙamin nasa ba.

Haka na zuwa kwanaki biyu da babban kwamandan Hisbah na Jihar Aminu Usman (Abu Amar) ya ajiye muƙamin sa.

By ukarofi

Leave a Reply