Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Masana kiwon lafiya sun yi gargaɗin cewa, irin abubuwan da ’yan Nijeriya ke ci, sha da kuma amfani da su a kullum su na ƙara zama babbar barazana ga lafiyarsu da rayuwarsu. Sun ce yawan cin abincin da aka sarrafa fiye da kima, shan abubuwan zaƙi, barasa, taba da kuma miyagun ƙwayoyi na ƙara jefa mutane cikin cututtuka masu tsanani, tare da lalata muhimman sassan jiki da kuma haddasa mutuwa da wuri.
Cututtuka masu barazana ga rayuwa kamar gazawar ƙoda, ciwon hanta mai tsanani, kansa, ciwon sukari da hawan jini na ƙaruwa a Nijeriya, inda masana kiwon lafiya suka ce salon rayuwa mara kyau na daga cikin abubuwan da ke ƙara dagula matsalar. A cewar masana, waɗannan cututtuka waɗanda a baya ake kallonsu a matsayin “cututtukan masu hannu da shuni”, yanzu sun mamaye kowane ɓangare na al’umma, suna raba iyalai da masu ciyar da su, tare da jefa gidaje cikin talauci da kuma ƙara wa tsarin kiwon lafiyar ƙasar da ke fama da ƙarancin kayan aiki nauyi.
Masana sun ce matsalar ba ta ta’allaƙa ne kawai da gado ba, domin abincin da ake ci, abubuwan da ake sha da kuma abubuwan da ake amfani da su kamar abincin da aka sarrafawa fiye da kima, barasa, taba, miyagun ƙwayoyi da abubuwan sha masu zaƙi na ƙara haifar da yaɗuwar cututtukan da ba sa yaɗuwa daga mutum zuwa mutum.
Tsohon Shugaban ƙungiyar Likitocin Nijeriya (NMA), Farfesa Francis Faduyile, ya danganta ƙaruwa da waɗannan cututtuka, musamman a tsakanin matasa, da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, amfani da magungunan gargajiya marasa inganci da kuma salon rayuwa mara kyau.
Faduyile ya ce, yawaitar samun magungunan zamani da na gargajiya tare da yin amfani da su ba bisa ƙa’ida ba na jefa muhimman sassan jiki cikin matsanancin haɗari.
Ya ce, kusan dukkanin magungunan da mutum ya sha suna ratsa ƙoda kafin a fitar da su daga jiki, sai kaɗan daga cikinsu da ake fitarwa ta bayan gida.
Ya ƙara da cewa, idan magani ya kasance mai cutar da ƙoda, zai iya haifar da lalacewar da ba za a iya gyarawa ba.
A cewarsa, sassauta dokokin da suka shafi magungunan gargajiya ta ƙara dagula lamarin, saboda wasu daga cikin magungunan da ake sayarwa a kan tituna da rumfunan kasuwa na ɗauke da sinadarai da ba a san su ba kuma za su iya cutar da jiki.
“Duk abin da muke ci ko sha yana ratsa muhimman gaɓoɓi biyu; hanta wajen sarrafa shi, da ƙoda wajen fitar da shi. Idan waɗannan abubuwa suna ɗauke da guba, za su iya haifar da lalacewar da ba za a iya gyarawa ba,” inji shi.
Dangane da lafiyar hanta, Faduyile ya ce kamuwa da cutar hanta mai yaɗuwa, wato hepatitis, na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa cututtukan hanta a Nijeriya.
Sai dai ya yi gargaɗin cewa shan barasa, amfani da miyagun ƙwayoyi da kuma magungunan gargajiya masu haɗari na ƙara sa lalacewar hanta da kansar hanta bayyana da wuri.
Ya ce hakan na haifar da “rauni sau biyu”, domin hantar da cutar hepatitis ta riga ta raunana na ƙara saurin lalacewa idan ana ci gaba da jefa mata abubuwa masu cutarwa.
Faduyile ya kuma yi gargaɗin cewa amfani da miyagun ƙwayoyi, ciki har da tramadol, maganin shaƙe da sauran abubuwan da doka ta haramta, na jefa zuciya cikin matsanancin aiki.
Ya ce wasu daga cikin waɗannan ƙwayoyi na sa zuciya bugawa da sauri kuma da ƙarfi, wanda a hankali zai iya haifar da hawan jini, gazawar zuciya da shanyewar ɓangaren jiki, waɗanda yanzu ake ƙara ganinsu a tsakanin matasa. Ya kuma ƙaryata ra’ayin cewa sigarin lantarki, wato shisha, ya fi na gargajiya aminci, yana mai cewa bincike ya nuna cewa shi ma yana da nasa illolin lafiya. A cewarsa, ko sigari ne, ko sigarin lantarki ko wasu abubuwan da ake shaƙa, suna shiga cikin jini, suna ƙara wa ƙwaƙwalwa da zuciya aiki fiye da kima, sannan daga baya su lalata muhimman gaɓoɓin jiki.
Faduyile ya yi kira da a gaggauta ɗaukar matakan kiwon lafiyar jama’a, ciki har da tsaurara dokokin kula da magungunan gargajiya da na zamani, ƙara yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi musamman tsakanin matasa, da kuma farfaɗo da shirye-shiryen rigakafin cutar hepatitis da sauran cututtukan da za a iya kare kai daga gare su.
Wani Likitan Cututtukan Hanta da Ciki a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abuja da ke Gwagwalada, Dakta Ameh Ojonugwa, ya ce shan barasa da amfani da magungunan gargajiya marasa cikakken tsari na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa cututtukan hanta. Ya ce wasu marasa lafiya na zuwa asibiti da mummunar lalacewar hanta bayan amfani da irin waɗannan magunguna, saboda ba su da ingantaccen tsarin ƙayyade adadin da ya dace a sha.
A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), cututtukan da ba sa yaɗuwa daga mutum zuwa mutum yanzu na haddasa mutuwar kusan mutum ɗaya cikin uku a Nijeriya.
Masana kiwon lafiyar jama’a sun ce wani babban haɗarin da ke ƙara ɓoye kansa shi ne yawaitar abubuwan sha masu zaƙi da abincin da aka sarrafa fiye da kima, waɗanda ake tallatawa sosai kuma mutane ke amfani da su a kullum. Sun ce irin waɗannan abubuwa na da alaƙa da kiba, cututtukan zuciya, ciwon sukari da mutuwa da wuri.
Abubuwan sha masu zaƙi sun haɗa da abubuwan sha da aka ƙara musu sukari ko wasu nau’o’in zaƙi kamar fructose, glucose, zuma da sucrose. Cikin su akwai lemun kwalba mai gas, abubuwan sha masu ƙara kuzari, madarar da aka ƙara mata zaƙi, shayi da kofi masu zaƙi da kuma wasu ruwan ’ya’yan itatuwa.
Farfesa Olukunmi Olaitan na Jami’ar Ilorin ya ce irin waɗannan abubuwan sha na samar da abin da ya kira “calories marasa amfani”, waɗanda za su iya haddasa ƙiba, ciwon sukari da cututtukan zuciya. Ya ce kusan kashi 30 cikin 100 na mace-macen Nijeriya na da alaƙa da cututtukan da ba sa yaɗuwa, da dama daga cikinsu kuma suna da alaƙa da rashin ingantaccen tsarin abinci.
Olaitan ya ce tsarin abincin ’yan Nijeriya na ƙara karkata zuwa abincin da aka sarrafa fiye da kima, wanda ke ɗauke da yawan sukari, kitse da gishiri, yana mai gargadin cewa hakan na ƙara yawan masu fama da hawan jini, shanyewar ɓangaren jiki, ciwon sukari da wasu nau’o’in kansa. Ya ce rashin ingantaccen abinci na da alaƙa kai tsaye da ƙaruwa a yawan masu fama da hawan jini, shanyewar ɓangaren jiki, ciwon sukari har ma da kansa.
Hawan jini, wanda ke daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa cututtukan zuciya, ya ƙaru sosai a Nijeriya, daga kashi 8.6 cikin 100 a shekarar 1995 zuwa kashi 32.5 cikin 100 a 2020, yayin da matsakaicin adadin da aka daidaita da shekaru ya kai kashi 38.1 cikin 100.
Masana sun danganta wannan ƙaruwa da abubuwa da dama, ciki har da yawan shan abubuwan sha masu zaƙi, gishiri da kitse marasa amfani. Nijeriya kuma na fuskantar babbar matsalar cutar kansa, inda ake samun sabbin masu kamuwa da cutar kusan 102,000 a kowace shekara, yayin da kimanin mutane 72,000 ke mutuwa sakamakon cutar a shekara.
Masana sun gano ƙiba, wadda rashin ingantaccen tsarin abinci ke iya haddasawa, a matsayin ɗaya daga cikin abubuwan da ke ƙara haɗarin kamuwa da wasu nau’o’in kansa.
Wani masanin kiwon lafiyar jama’a, Dakta Joseph Ekiyor, ya ce cin abinci mai gina jiki na taimakawa wajen daidaita hawan jini, sukarin jini da sinadarin cholesterol, tare da rage haɗarin bugun zuciya da shanyewar ɓangaren jiki.
Ekiyor, wanda ya yi nuni da shawarwarin WHO, ya ce sikarin da ake ƙarawa cikin abinci ya kamata ya kasance ƙasa da kashi 10 cikin 100 na jimillar kuzarin da mutum ke samu a rana, yayin da rage shi zuwa ƙasa da kashi biyar zai iya ƙara inganta lafiya. Ya kuma ba da shawarar cewa kitse bai kamata ya wuce kashi 30 cikin 100 na kuzarin da mutum ke samu a rana ba, yayin da ya kamata a taƙaita gishiri zuwa ƙasa da gram biyar a rana.
Ya kuma shawarci ’yan Nijeriya su riƙa cin aƙalla giram 400 na ’ya’yan itatuwa da kayan marmari a kowace rana. Ya ce hatsi cikakke, wake da sauran nau’o’in kayan lambu, ƙwayoyi da abincin da ba a sarrafa ba ya kamata su kasance ginshiƙin ingantaccen tsarin abinci.
Yawan shan lemun kwalba na ƙara barazana:
ƙungiyar ɗaukar Matakan Rage Shan Sukari ta ƙasa, wato National Action on Sugar Reduction (NASR), wadda ta hada ƙungiyoyin kiwon lafiya, ta ce Nijeriya na cikin ƙasashen duniya da suka fi yawan shan abubuwan sha masu zaƙi. A cewar ƙungiyar, Nijeriya ta kasance ta huɗu a duniya wajen yawan shan lemun kwalba a shekarar 2019, sannan ta kasance ta bakwai wajen yawan shan abubuwan sha masu iska idan aka kwatanta da yawan mutum.
ƙungiyar ta kiyasta cewa kowane mutum yana shan kusan kwalabe 498 na girman oza takwas a shekara. Ta kuma kiyasta cewa ana sayar da lita miliyan 38.7 na abubuwan sha masu zaƙi a Nijeriya a kowace shekara, tana mai cewa yawan shan su na ƙara wa matsalar cututtukan da ba sa yaɗuwa daga mutum zuwa mutum nauyi.
NASR ta ce ’yan Nijeriya na kashe kusan dala miliyan 4.5 a shekara wajen maganin ciwon sukari, tana mai cewa ciwon sukari ɗaya ne kawai daga cikin cututtukan da ke da alaƙa da rashin ingantaccen abinci da salon rayuwa. Ta ƙara da cewa, cututtukan da ba sa yaɗuwa, ciki har da ciwon sukari, ƙiba da cututtukan zuciya, na haddasa kusan kashi 29 cikin 100 na mace-macen Nijeriya.
Ma’aikatar Lafiya da Jin Daɗin Jama’a ta Tarayya ta taɓa bayyana damuwa kan ƙaruwa da matsalolin lafiya da ke da alaƙa da abubuwan sha masu zaƙi, musamman kiba da ciwon sukari. Ministan Lafiya da Jin Daɗin Jama’a mai Kula da Ayyukan Ma’aikatar, Farfesa Muhammad Ali Pate, ya ce ƙaruwa da cututtukan da ke da alaƙa da abubuwan sha masu zaƙi na ƙara matsin lamba kan tsarin kiwon lafiya, yayin da kuɗaɗen magani ke ƙaruwa sosai.
Shaye-shayen miyagun ƙwayoyi:
Nijeriya na fuskantar babbar matsalar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, inda Ma’aikatar Lafiya da Jin Daɗin Jama’a ta Tarayya ta kiyasta cewa kashi 14.4 cikin 100 na mutanen da shekarunsu ke tsakanin 15 zuwa 64 na amfani da miyagun ƙwayoyi. Wannan adadi na nufin kusan ’yan Nijeriya miliyan 14.3 a cikin wannan rukunin shekaru.
Tsohon Darakta a ma’aikatar, Dakta Chukwuma Anyaike, ya ce kusan mutane miliyan uku daga cikin waɗanda abin ya shafa na fama da matsalar dogaro da miyagun ƙwayoyi. Ya ce mata na da kusan kashi ɗaya cikin huɗu na masu amfani da miyagun ƙwayoyi, wato kimanin mata miliyan 3.5. Anyaike ya kuma bayyana cewa sama da kashi 40 cikin 100 na mutanen da aka ware a matsayin masu yawan amfani da miyagun ƙwayoyi na buƙatar magani, amma ba sa samun damar yin amfani da ayyukan da suka dace.
Darakta-Janar na Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta ƙasa (NAFDAC), Farfesa Moji Adeyeye, ta ce illolin samarwa da amfani da miyagun ƙwayoyi sun wuce mutanen da ke amfani da su, domin suna da tasiri ga iyalai, al’umma da tattalin arzikin ƙasa.
Ta ce tabar wiwi ce aka fi amfani da ita cikin miyagun ƙwayoyin da doka ta haramta a Nijeriya. A cewarta, kimanin kashi 10.8 cikin 100 na al’ummar ƙasar, wato kusan mutane miliyan 10.6, sun taɓa amfani da tabar wiwi cikin shekara guda da ta gabata.
Adeyeye ta ce matsakaicin shekarun da mutum ke fara amfani da tabar wiwi a cikin al’umma shi ne shekara 19, abin da ta ce na ƙara nuna haɗarin fara amfani da miyagun ƙwayoyi tun da wuri da kuma illolinsu na dogon lokaci.
Taba na lalata kusan kowane sashe na jiki:
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi gargaɗin cewa amfani da taba na cutar da kusan dukkanin gaɓoɓin jiki, kuma yana da alaƙa da cututtuka masu barazana ga rayuwa, ciki har da kansa, cututtukan zuciya da na hanyoyin numfashi. Bayanan shekarar 2018 sun nuna cewa ’yan Nijeriya sun sha fiye da sandunan sigari biliyan 20 a shekara, yayin da aka kiyasta cewa amfani da taba na haddasa mutuwar kusan mutane 30,000 a kowace shekara.
Babban Likitan Cututtukan Huhu na ƙasa a Asibitin ƙasa da ke Abuja, Dakta Kingsley Osagie, ya ce shan taba na ƙara haɗarin kamuwa da cututtukan hanyoyin numfashi, ciki har da kumburin hanci da kogon hanci, ciwon maƙogaro mai ɗorewa, yawan kamuwa da ciwon asma da kuma cutar toshewar hanyoyin numfashi ta dindindin (COPD).
A cewarsa, masu shan taba na cikin haɗarin kamuwa da nau’o’in kansa da dama, musamman kansar leɓɓa, harshe, maƙogaro da huhu. Ya ce hayakin taba na ɗauke da sinadarai sama da 7,000, kuma aƙalla 250 daga cikinsu an tabbatar da cewa na iya haddasa kansa.
Osagie ya kuma yi nuni da wasu illolin taba da ba a cika magana a kansu ba, inda ya ce shan taba na iya lalata ƙwayar pancreas tare da ƙara haɗarin kamuwa da ciwon sukari. Ya ƙara da cewa, illar taba ga jijiyoyin jini na iya ƙara haɗarin hawan jini da sauran matsalolin cututtukan zuciya. Illar taba ba ta tsaya ga lafiya kawai ba, domin tana da babban tasiri ga tattalin arziki.
Wani binciken da aka wallafa a shekarar 2023 a mujallar Population Medicine, mai taken Economic burden of tobacco consumption in Nigeria, 2013–2020, ya nuna cewa Nijeriya na ɗaukar babban nauyin kuɗaɗen da cututtukan da taba ke haddasawa ke jawo wa ƙasa.
Binciken ya kiyasta cewa cututtukan da suka shafi taba sun cinye wani kaso mai yawa na kuɗaɗen kiwon lafiya na Nijeriya cikin shekaru takwas. Taba da ake shaƙa ta kasance mafi yawan kaso na wannan nauyi, inda aka kiyasta kuɗaɗen da ta haddasa sun kai dala biliyan 9.37, yayin da taba da ba a shaƙa ba ta ƙara dala miliyan 749.66.
Gaba ɗaya, binciken ya kiyasta jimillar nauyin tattalin arzikin amfani da taba a Nijeriya da kusan dala biliyan 9.45 tsakanin 2013 zuwa 2020, kwatankwacin kusan kashi 0.28 cikin 100 na Jimillar Kayayyakin da ƙasa Ke Samarwa (GDP) a wannan lokaci.
Barasa ma na ƙara barazanar:
ƙididdigar da ake da ita ta nuna cewa yawan barasar da aka yi wa rajista da ake sha a Nijeriya ya kai kusan lita 3.78 na barasa tsantsa ga mutum ɗaya a shekarar 2020. Sai dai alƙaluman da suka dogara da sayar da barasar da aka yi wa rajista kaɗai ba lallai su nuna ainihin yawan barasar da ake sha ba, saboda ba sa ɗaukar barasar da ake samarwa a gida ko wadda ba a yi mata rajista ba.
Binciken baya ya kuma nuna bambanci wajen shan barasa tsakanin maza da mata da kuma tsakanin mutanen birane da karkara, inda aka ce shaye-shayen barasa masu cutarwa sun fi yawa a yankunan karkara fiye da birane. Binciken Kiwon Lafiya da Demography na Nijeriya na shekarar 2024 (NDHS) ya ƙara nuna bambancin jinsi, inda ya gano cewa yawan shan barasa tsakanin mazan Nijeriya masu shekaru 15 zuwa 49 ya ninka na mata fiye da sau biyu.
Wannan na da muhimmanci saboda bayanan duniya sun nuna cewa maza na ɗaukar babban kaso na mace-macen da barasa ke haddasawa. WHO ta ce barasa ce ta haddasa kashi 6.7 cikin 100 na dukkan mace-macen maza a duniya a 2019, idan aka kwatanta da kashi 2.4 cikin 100 na mata.
Hukumar ta ce illar barasa ga lafiya ba ta dogara da yawan abin da mutum ya sha kawai ba, har ma da yadda yake shan barasar, yawan lokutan da yake sha da kuma adadin da yake sha a lokaci guda. Ta ce mafi yawan illolin da barasa ke haddasawa na faruwa ne sakamakon yawan shan barasa a lokaci guda ko kuma yawan shan ta a kai a kai.
ƙaruwa da ƙiba, hawan jini, ciwon sukari, kansa da sauran cututtukan da ba sa yaɗuwa daga mutum zuwa mutum na ƙara bayyana illolin salon rayuwa mara kyau a Nijeriya. Daga yawan cin abincin da aka sarrafa fiye da kima da shan abubuwan sha masu zaƙi, zuwa barasa, taba da miyagun ƙwayoyi, zaɓin da mutane ke yi a rayuwarsu ta yau da kullum na ci gaba da yin mummunan tasiri ga lafiyar ’yan Nijeriya da ƙarfin aikinsu.
Haka kuma, wannan matsala na ƙara wa iyalai nauyin kuɗaɗen magani tare da ƙara matsin lamba kan tsarin kiwon lafiya da tuni yake fuskantar ƙalubale. ɗaukar matakan rage waɗannan haɗurran da ke da alaƙa da salon rayuwa tun yanzu na iya taimakawa wajen rage mace-macen da za a iya kauce musu, rage kuɗaɗen kiwon lafiya da kuma samar da al’umma mai ƙoshin lafiya a shekaru masu zuwa.
