Topfeed ta yi taro da ‘yan kasuwa da manoma kan abincin kaji masu ƙwai

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano 

Kamfanin Premier Feed Mills masu yin abincin dabbobi na Topfeed, ta gudanar da taro a jihar Kano da dillalan abincin dabbobi da ‘yan kasuwa da masu kiwon kaji ta gabatar musu da sabon dusar kaji  masu ƙwai ” Lawyer wise’ da suka samar.

Mista Choji Fabian manajan  kasuwanci  mai kula da shiyyar Arewa maso yamma na kamfanin ya ce maƙasudin gabatar da abincin kajin masu yin ƙwai “Lawyer wise'” don taimakawa masu kiwon kaji ne da abinci mai rahusa da auki da zasu riƙa samar musu da kwai akan kari kuma na tsawon shekaru idan an lura dasu da kyau .

Ya ce “Topfeed “suna yin abincin dabbobi da kaji da kifi sama da shekaru 20 shi yasa da suka fito da sabon samfurin abincin kaji na masu yin ƙwai suka gayyaci abokan hulɗar su da sauran mutane masu kiwo harma adadin mutane da suka yi tsammanin zasu zo sun fi haka  an sami nasara.

Mista Choji Fabian manajan kasuwanci  kula da shiyyar  Arewa maso yamma ya ce suna fata abincin kaji masu ƙwai ya sami karɓuwa saboda sauƙin farashi da  aka samu sakamakon kayan abinci da ake sarrafa abincin kaji ya ɗan sauko don haka suka sauƙaƙa abincin kajin da suke fata masu kiwo zasu sami biyan buƙata.

Shi ma shugaban Kamfanin Albarka poultry serɓices.Alhaji Yaƙub Ibrahim ya bayyana kaddamar da sabon abincin kajin da Topfeed suka yi zai baiwa manoman kaji cigaba musamman halinda ake ciki na tsadar kaya an samar da sabon samfurin abincin kajin da zai bada fa’ida.

Shi ma manajan  kamfanin  gudanarwa  na Albarka poultry kuma me Kamfanin  U.I. Nasiha  Alhaji  Umar Ibrahim ya yaba da yanda Topfeed ke samar da abincin dabbobi kuma ita kaza bata fiye jurewa yanayi na canje canje ba shi yasa aka ƙaddamar da wannan abincin kajin a wannan lokaci da ake samun sauyi domin manoma su sami fa’idar abinda take ɗauke da shi.

By ukarofi