Kwanaki 12 a wa’adin mulkinsa na biyu, Shugaba Donald Trump ya ba da umarnin kai gaggarumin farmakin soji kan ƙungiyar ISIS da Somaliya, a wani mataki da jami’ai suka ce yana nuni da ƙudurinsa na kawar da barazanar ta’addanci.
Rundunar sojan Amurka ta Afrika (AFRICOM) a ƙarƙashin jagorancin sabon sakataren tsaron da aka rantsar, Pete Hegseth, ta kai wani harin samame ta sama a tsaunin Golis na Somalia, inda rahotanni suka ce sun kashe wasu mayaƙan ISIS.
Jigon ɗaukar matakin na gaggawa dai shi ne yadda shugaba Trump ya mayar da hankali kan barazanar da wungiyar ISIS ke yi, musamman masu alaƙa da su a Afirka. A cikin wata sanarwa da ya fitar, Mista Hegseth ya bayyana cewa, “Bisa umarnin shugaba Trump da kuma haɗin gwiwa da gwamnatin tarayyar Somaliya, mun bai wa rundunar sojojin Amurka izinin gudanar da hare-hare ta sama a yau kan mayaƙan ISIS da Somaliya a tsaunin Golis.”
Wannan saƙon na nuni da ƙudurin Mista Trump na yaƙi da ta’addanci da kuma shirinsa na ɗaukar matakai cikin gaggawa dangane da barazanar da duniya ke fuskanta.
An ba da izinin kai harin ta sama ne mako guda bayan an rantsar da Mr Hegseth a matsayin sakataren tsaro na 29, wanda ke zama ɗaya daga cikin muhimman shawarwarin da ya yanke game da matakin sojan Amurka a Afirka.
Saurin shigar da Mista Hegseth ke yi yana nuni da zafin naman sa wurin yaƙi da ta’addanci. Idan aka kwatanta, a baya AFRICOM ta sha kai hare-hare a lokacin wasu gwamnatoci, amma saurin da kuma kai tsaye da Mista Hegseth da Shugaba Trump suka yi kan wannan barazanar ISIS ya sanya wani sabon salo. Yayin da Ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta yi saurun bayyana sakamakon wanda ya ƙara bayyana sabon salon gwamnatin da ke yanzu.
Sanarwar da ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta fitar game da harin ta tabbatar da nasarar harin yayin da AFRICOM ta sake jaddada aniyar ta na kaucewa cutar da fararen hula, yana mai cewa, “Rundunar Sojojin Amurka da na Afirka na ɗaukar manyan matakai don hana cutar da fararen hula. Kare fararen hula ya kasance wani muhimmin ɓangare na ayyukan rundunar don inganta tsaro da kwanciyar hankali a Afirka.”
Wannan kuwa na da muhimmanci, yayin da yake nuni da cewa, matakin soja na ɗaya daga cikin muhimman manufofin Amurka a yankin, saidai har yanzu akwai gagarumin yunƙuri da ya kamata a yi na kaucewa hasarar rayukan fararen hula, ƙalubalen da ya dagula ayyukan soji a Afirka.