
Daga BELLO A. BABAJI
Babban Mai taimaka wa Shugaban Ƙasa akan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga ya ce nan ba da jimawa ba ƴan Nijeriya za su ga sauƙin al’amura a yayin da gyare-gyare a harkar tattalin ke fara aiki a ƙasar.
Onanuga a yayin ganawa da manema labarai a Legas, ranar Lahadi, ya ce kwanan nan tsare-tsaren Tinubu za su fara aiki a kowane fanni a Nijeriya.
Ya ce, ba kaɗai gabatar da sauye-sauye na ci-gaba Shugaba Tinubu ya yi ba, har ma da magance ƙalubalen da gwamnatocin baya suka ƙaurace wa, waɗanda suke hana ruwa gudu a yayin gudanarwa.
Ya kuma ce, shekaru biyu kaɗai ba za su wadatar ba wajen auna nasarorin da gwamnatin ta samu, yana mai cewa ƙwararru masu sharhi akan tasirin tsare-tsare akan al’umma suna ƙaddara shi ne daga shekara 10 zuwa 12.
Kakakin Shugaban ƙasar ya ƙara da cewa, gwamnatin Tinubu ta yi kwaskwarima a fannoni daban-daban wajen tabbatar da samun ci-gaba don amfanin ƙasar da al’ummarta.
Haka kuma, ya bayyana cewa, duk da matakan gwamnatin a shekaru biyu da suka gabata, an samu ci-gaba a harkar tattali duba da yadda ya magance matsaloli da dama, waɗanda a yanzu babu su, inda ya bada misali da gabannin cire tallafin fetur ana samun gidajen mai suna cewa babu fetur, lamarin da a yanzu kuma ba haka bane.
Kazalika, ya yi tsokaci game da rancen kuɗi da gwamnatin ke yi daga waje inda ya ce duk da cewa ƙasar tana da albarkatu masu tarin yawa, akwai ayyukan da sai an ranto kuɗi kafin a aiwatar da su kamar manyan tituna da makamansu, yana mai cewa Amurka ma ta kan karɓi aron kuɗi da sauran ƙasashen duniya.
Akan rugujewar Naira kuwa, Onanuga ya ce hakan abu ne gama-gari a duniya duba da tsarin harkokin tattalin arziƙi, wanda hatta ƙasashen Birtaniya da Amurka sun fuskanci irin hakan.
Bugu da ƙari, ya ce gwamnati tana ɗaukar matakai masu tsari ne domin faɗaɗa damanmakin ta ci-gaban ababen more rayuwa, inda ya bada misali da ayyukan manyan tituna, waɗanda ba sa cikin kasafi da fari.
