Benue: ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da fasinjoji tara a Bus

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Ƴan bindiga a Jihar Benue sun yi garkuwa da fasinjoji guda tara har da direban motar kamfanin sufuri na jihar a hanyar Owukpa zuwa Orokam dake Ƙaramar Hukumar Ogbadibo.

Lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 7 na yammacin ranar Asabar a yayin da fasinjojin ke dawowa daga kasuwar Orba ta Jihar Enugu zuwa Owukpa.

Wata ƴar Owukpa mai suna Grace Ogwuche ta shaida wa manema labarai cewa ƴan bindigar sun harbi direban da kuma ɗaya daga cikin fasinjojin a yayin harin.

Haka kuma wani fasinja da ya samu raunuka a sakamakon harbin da maharan suka yi masa, an garzaya da shi wani asibiti a garin Okpoga dake Ƙaramar Hukumar Okpokwu.

Shugaban ƴan banga a Owukpa, Amos Agada ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce ƴan bindigar ba su kira kowane ɗaya daga cikin iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su ba.

Ya kuma ce, jami’an tsaro sun fara aikin ceto fasinjojin da aka sacen.

By Babaji