Haƙiƙa Sheikh Ahmad Gumi jarumi ne

Spread the love

Daga ALI ABUBAKAR SADIK

Wato a ganina babu jarumta a duniya wadda ta kai mutum ya gane gaskiya kuma ya fito ƙarara ya nuna wa duniya hakan.

Kowa ya san cewa, Marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi ne ya kawo Izala Nijeriya. Da taimakon Sardaunan Sokoto, Sir Ahmadu Bello, ya ƙulla kyakkyawar alaka da ƙasar Saudiyya a lokacin da har Gwamnatin Arewa a ƙarƙashinsa na iya tallafa wa Saudiyya, domin akwai labarin da ke cewa, shi Sardaunan ya bayar da gudunmuwa ta kuɗaɗe, domin tallafa wa Saudiyya ta gina babban titin da ya tashi daga Makka zuwa Madina a wancan lokaci. Saudiyya a shekarun 1960s ta bijiro da yaɗa addinin Musulunci a ƙasashen duniya, kuma hanya ta farko da suka runguma ita ce ta lalubo malamai masana harsuna daban-daban na duniya, domin fassara Alƙur’ani a sauran yarukan duniya.

ƙungiyar Rabida (Muslim World League), wacce Sardaunan ya bayar da gudunmuwa wajen kafa ta, ta fara lalubo malamai masu fassara daga sassa na duniya, yayin da Sardaunan ya bayar da sunan Sheikh Abubakar Gumi, domin ya fassara ƙur’ani da Hausa. Ta haka ne ƙasar Saudiyya ta fara yaɗa Musulunci ta mahangar Wahabiyanci a ƙasashen duniya.

Izala ta kawo gagaruman canje-canje ta fuskar addini da zamantakewa a Arewacin Nijeriya, masu kyau da akasin haka. Manyan abokan gabar Izala da farko su ne ɗariku kafin a shekarun 1980 Shi’a ta fara karɓuwa.

ƙiyayya tsakanin Izala da Shi’a ta yi ƙamari ne sosai bayan wucewar Marigayi Abubakar Gumi, amma Dr Ahmad Gumi, ya wayi gari a gaba-gaba wajen yaƙar ’yan Shi’a. A baya kusan duk tafsirinsa za ka ga irin yadda ya ke far musu da wa’azi mai tsananin zafi a kan ’yan bidi’a.

Tsatstsauran ra’ayi na Wahabiyanci, a kowane sashe na duniya, za ka tarar cewa, gyauron yan Izala ne ke rungumar ta’addanci, domin yaɗa Musulunci ko kare shi ta hanyoyin Takfir (kafirta Musulmi) ko jihadi ta hanyar ta’addanci. An sami ƙungiyoyi irinsu Al-ƙaeda, ISIS, Al-Shabbab da namu irinsu Boko Haram. Dukkan waɗannan ƙungiyoyi, akasarin mambobinsu za ka samu gyauron koyarwar Wahabiyanci ne da ke amfani da wasu ayoyi da hadisai wajen halasta jinin mutane daban-daban.

A baya-bayan nan, Sheikh Ahmad Gumi ya sassauta daga tsananin da yake da shi a baya game da sauran ’yan uwa Musulmi, musamman ’yan Shi’a, domin har ya amsa gayyata zuwa Iran taron malamai kuma bayan dawowarsa ya fara kiran Musulmi su haɗa kai. Ya yi ƙoƙarin shiga sulhu da ’yan ta’adda da nuna buƙatar tattaunawa fiye da cewa a nuna ƙarfi. Sannan da bayyana cewa, ruhin matsalar a wajen ’yan ta’addan shine jahiltar Musulunci, wanda dole a koyar da su.

Kwanan nan, ƙasar Saudiyya ta hana shi shiga ƙasarta aikin Hajji, kuma idan ba mu manta ba a baya har tsare shi suka yi kafin su koro shi Nijeriya. Waɗannan abubuwa na faruwa ne sakamakon Ahmad Gumi ya fanɗare wa fahimtar kuskure ta Wahabiyanci da ya danganci abubuwa irin su yaƙi da ’yan Shi’a, yarda da tunani akan mas’aloli na addini, rarrabuwa da kuma bin wasu hadisai ido rufe, ko ɗabbaƙa su daidai da ƙur’ani, har ma da sauran abubuwa da su ka shafi siyasar gabas ta tsakiya, musamman rikicin Falasɗinawa da Isra’ila da sauran Musulmin duniya.

Waɗannan dalilai ne suka saka Saudi Arabia ta yi hannun riga da Ahmad Gumi, kuma haƙiƙa ya zama jarumin gaske wajen kasancewa malami da ya yarda ya tsaya akan ijtihadinsa tare da kaucewa duk abinda ya fuskanta ba daidai ba ne. Wannan ya janyo masa gaba, ba daga Saudiyya kaɗai ba, har ma daga cikin ’yan uwansa yan Izala a nan Nijeriya, yadda magoya bayan wani sashe nasu ke cin zarafinsa da munanan kalamai.

Fatanmu dai shine Allah ya ci gaba da haɗa kan Musulmi kuma ya ƙaro mana malamai a wannan al’umma irinsu Dr Ahmad Gumi, waɗanda ba sa tsoron tsayawa kan gaskiya, kuma mu gane cewa, ita gaskiya har abada ba ta samuwa sai ka yi wa ƙarya bara’a. Kuma mu gane cewa, duk wata hayaniya da muke fuskanta a matsayinmu na Musulmi a yau a duniya, shine sakamakon bijire wa umarnin Allah cewa, “Fa a’tasimu bi hablillah jamia.”

Malam Ali Sadiƙ manazarci ne kuma marubuci a Kano

By ukarofi