Tsarin NBT na bai wa kanikawa shaidar ƙwarewa har matakin farfesa abin yabo ne – Shugaban KASTMOMA

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

An bayyana cewa tsarin gwada kanikawan baki titi na basu takardar shaidar karatu a makaranta daidai gwargwadon ƙwarewa da basirar ka ta fanni da ka ƙwarewa a kanikanci abin ne da zai kawo cigaba a wannan fanni da ma Nijeriya baki ɗaya, kamar dai yadda shugaban Kano State Tricycle, Motorcycle Mechanic Association Injiniya Muhammad Abdullahi Usman shugaban KASTMOMA ya bayyana a wannan lokaci.

Ya ce tsarin hukumar kula da makarantun fasaha NBT ta Nijeriya ta ɓullo da wani wanda wani kwamiti zai ziyarci bakanike a bakin titi ya gwada shi kuma a ba shi takardar shaidar da ta dace da shi tun daga mataki na ɗaya na biyu na uku har matakin farfesa zai iya samu kuma duniya ta amince da wannan tsarki wannan abin a yaba ne cewar shugaban KASTMOMA na Kano.

Haka kuma Injiniya Muhammad Abdullahi Usman ya bayyana cewa wannan ƙungiya ta su ta samu cigaba wanda ta horar da matasa sama da 2000 da goyon bayan ƙungiyoyi da hukumomin gida da na wajen Nijeriya irinsu NOS, DFD, ITF da sauransu a lokuta daban-daban, kuma wannan ƙungiya tana aiki ne domin horar da matasa da sama musu aikin yi wanda zai hana su zaman banza da harkar shaye-shaye da duk wani abu da zai gurɓata tarbiyyar matasa a wannan lokaci.

A ƙarshe Injiniya Muhammad Abdullahi Usman ya yaba wa tsohon gwamnan Kano Injiniya Dakta Rabiu Musa Kwankwaso wanda shi ya asassa wannan ƙungiya ta hanyar haɗe masu wannan sana’ar waje ɗaya a shekarar 2014 inda ya haɗa ɗaukacin masu wannan sana’ar a cibiyar horar da matasa ta Sani Abacha daga ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano aka ɗauki nauyinsu wajen ciyarwa na kwana da kwanaki kuma waɗanda suka zo daga nesa aka basu wurin kwana da abinci mai kyau sau uku a rana bayan kammalawa aka bai wa kowa kayan aiki da motoci da kuma kuɗin alawus na 20,000 tun a waccen lokacin, haka shi ma zuwan gwamna Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje a wannan ƙoƙari da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ƙirƙirar mana shi ma abun a yaba musu ne ga kuma yanzu wannan gwamnan Alhaji Abba Kabir Yusuf shi ma muna yaba masa da yadda ya ke ƙokarin taimaka mana kan wannan sana’a tamu ta gyaran babur mai ƙafa biyu da me kafa uku a wannan jiha tamu ta Kano.

By ukarofi