Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Alhaji Muhammad Inuwa Labaran, Sarkin Kasuwar waya ta Berut da ke Kano, ya nemi al’ummar jihar da Nijeriya baki ɗaya kan a cigaba da addu’a wajen samun dawwamammen zaman lafiya a Kano da kuma samun tsaro da zaman lafiya a wasu jihohi da suke fama da matsalar tsaro a Nijeriya da kuma samun dawwamammen zaman lafiya a Nijeriya baki ɗaya, musamman a wannan lokaci na bukukuwan babbar salla, inda ya ce akwai buƙatar a cigaba da bai wa hukumomin Nijeriya haɗin kai domin zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Haka kuma ya ce akwai buƙatar addu’a domin Allah ya karɓi ibadun mu na layya da sauran azikaru da ake yi a waɗannan kwanaki na Zul-Hajji da kuma zikirin da ake yi bayan saukowa daga sallar Idi domin neman yardar Allah, Allah ya karɓa mana ibadu baki ɗaya.
Haka kuma Sarkin Kasuwar waya ta Berut ya yi amfani da wannan dama wajen yaba wa gwamnatin Kano kan irin ƙoƙarin da take yi na gyaran tituna a birnin Kano da kewaye ga kuma abin da ta yi na biyan tsofaffin kansiloli haƙƙinsu wanda ana ganin hakan zai sa tsofaffin kansilolin su yi sallah su da iyalan su cikin walwala kamar yadda ya kamata ga kuma biyan ‘yan fansho kuɗin garatuti da dai sauran abubuwa na kyautatawa mutane wanda ake buƙatar kowanna shugaba a kowanna mataki na mulki yayi ƙokarin kyautatawa alumma abin ne mai kyau.
A ƙarshe Sarkin Kasuwar Alhaji Muhd Inuwa Labaran, ya yi nasiha ga ‘yan kasuwar waya ta Berut da sauran ‘yan kasuwa da su ƙara jajircewa wajen inganta kasuwanci ta hanyar ƙwazo da kuma kyakkyawar mu’amala da abokan ciniki dama sauran al’umma baki ɗaya a ta bakin ɗaya daga cikin sarakuna kasuwanni da suke a matsayin iyayen al’umma ba ‘yan siyasa ba.
