Yadda ‘yan bindiga suka kashe mutum 25 a hare-haren Benuwai

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Rahotanni daga jihar Benue da ke Arewa ta Tsakiyar Nijeriya na bayyana cewa fiye da mutum 25 aka hallaka a hare-haren da aka kai wasu ƙananan hukumomin jihar yayin da wasu da dama suka jikkata.

An kai hare-haren ne a ƙauyukan Ankpali da Naka a jihar da ke fama da rikicin da ya ƙi ci, ya ƙi cinyewa tsakanin makiyaya da manoma.

A harin farko a safiyar Lahadi, akalla mutum 14 aka kashe a ƙauyen Ankpali da ke ƙaramar hukumar Apa, a cewar shugaban ƙaramar hukumar Adam Ochega kamar yadda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Mista Ochega ya kuma yi gargaɗin cewa ana ci gaba da samun barazanar wasu hare-haren a yankin.

An sake kai wani harin a yammacin ranar Lahadin, inda aka kashe aƙalla mutum 16, tare da jikkata da dama a ƙauyen Naka da ke karamar Gwer ta Yamma.

Wata mazauniyar yankin ta shaida wa BBC cewa suna zaune a gida da misalin ƙarfe 7:00 na yamma sai ga mutanen sun shigo garinmu sun harbi kan kowa da kowa.

”Kuma sun ci gaba da harbe-harbe har ƙarfe 1:00 na dare, kuma bayan zuwan jami’an tsaro sun guda, bayan guduwarsu an tattaro gawa 16,” a cewarta.

Rahotanni na bayyana cewa ko a watan da ya gabata ma, mutum 44 aka kashe cikin kwana huɗu a ƙaramar hukumar Gwer ta Yamma.

Zuwa yanzu dai ba a san makasudin kai hare-haren ba, sai dai shugaban karamar hukumar Gwer ta yamma Ormin ɓictor a tattaunawarsa da AFP, ya zargi fulani makiyaya da kai hare haren.

Sai dai a gefe guda kuma makiyaya a yankin na zargin cewa ana kai musu hare-hare tare da ƙwace musu filaye da kuma sanya wa dabbobinsu guba.

‘yan sandan jihar sun tabbatar wa kamfanin dillancin labaran na AFP cewa an kai hare-haren, sai dai ba su faɗi adadin mutanen da abin ya ritsa da su ba.

Jihar ta Benue da ke tsakiyar Nijeriya dai na fama da irin waɗannan hare-hare da na ramuwar gayya sakamakon rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya, inda rahoton baya bayan nan na ƙungiyar Amnesty Internationa ya nuna cewa akalla mutum 6,800 aka kashe a jihar cikin shekara biyu.

By ukarofi