Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
An bayyana cewa yadda taron horar da kanikawa masu gyaran ababen hawa da MD Global Sight ya gayyaci ƙungiyar NATA wato Nigerian Artisans Technician Association reshen jihar Kano ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar reshen jihar Kano Kwamared Yahaya Ibrahim kuma shugaban ƙungiyar masu gyara KATFO Kano Technician Forum wanda shi ne shugaban waɗannan ƙungiyoyi guda biyu na ƙasa reshen jihar Kano ya bayyana cewa yadda wannan Global Sight ya gayyace su na cewa za a horar da su harkar zamani da ake kira CNG na yadda za a canza injina masu aiki da man fetur zuwa daidai da abin da ya shafi iskar gas da sauran ilimi na sabuntawa da bunƙasa sana’o’in su na zamani to kuma su ka ga gaskiya ba haka abin yake ba, domin kuwa abun da ya basu mamaki da ban haushi shi ne wanda aka gayyato ya basu ilimin menbar ne a wannan ƙungiya ta NATA kuma a ganina ba shi da wani ilimi saboda zai bamu a matsayin mu waɗanda muka koyi wannan sana muna yin ta shekara da shekaru kamar dai yadda shugaban NATA Kwamarede Yahaya Ibrahim ya bayyana wa manema labarai bayan taron ya tashi ba tare da wata biyan buƙata ba.
Haka kuma Malam Yahaya Ibrahim ya ce: “Global Sight ƙarƙashin shugabancin Dayo Bello ya gayyace mu ya ce mu bashi mutane koda sama da dubu 2 zaa horar da su a wannan aikin dai dai zamani amma da aka zo taron duk abinda aka faɗa na koyarwa bamu ganshi ba kuma haka aka taramu daga ƙananan hukumomi 44 na Kano dai dai da ruwan sha ko abinci sai dai kazo da kayan ka wannan abu ne da baimana daɗi ba hakan ta sa mun nemi jin ta bakinsa a matsayina na shugaban NATA amma aka kasa fahimtar juna aka tashi baran baran ba tare da mu da aka gayyato buƙatar mu ta biya bah aka dai aka tashi, to sai muke ganin cewa ita kanta gwamnatin Kano ƙarkashin shugabanci Alhaji Abba Kabir Yusuf mai ƙaunar mutanan Kano da kishin Kanawa bata san yadda wannan abin ya kasance ba domin kuwa muna ganin ita ma an yaudare ta ne akan wannan taron horarwa da aka shiryawa NATA da sauran ɗinbun ƙungiyoyi masu sanaoi a Kano wanda muke kira ko shawara kan abinciki wannan Global Sight ƙarkashin shugabanci Dayo Bello domin tattance gaskiyar lamarin abin da ya faru a wannan horo da aka shiryawa Kanawa wanda muke ganin ‘yan burun-burun ne kawai.”
Kwamarede Yahaya Ibrahim ya ce, tun da farko shugaban Global Sight ya tabbatar wa ƙungiyar mu ta NATA cewa sun nemi gwamnatin Kano ta basu taimakon ɗaukar nauyin wurin taro da abin zama da tsaro kuma gwamnatin Kano ta ɗauka ta kuma yi wanda hakan ce ta sa ya ce mu tura menbobin mu ko da sama da dubu 2 ne babu matsala banda kuma sauran ƙungiyoyi masu kama da namu haka muka tura amma babu biyan buƙata a cewar shugaban NATA na ƙasa reshan jihar Kano.
Haka kuma shugaban NATA yayi bayanin yadda tsohon gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya shirya musu taron horarwa na gaskiya suka ci suka sha a wadace kuma aka koya musu aiki aka basu kayan aiki aka basu kuɗi na tallafi domin bunƙasa sanaoin su a lokacin da ya sa gwamna Kano, kuma shi ma wannan gwamnan Alhaji Abba Kabir Yusuf yana da kishin wannan ƙungiya ta NATA kamar yadda ya ke da kishin alummar Kano baki ɗaya.
Shi ma a jawabin sa ga manema labarai shugaban Global Sight Dayo Bello ya ce wannan kamfanin su na aiki ne domin taimakawa irin waɗannan ƙungiyoyi domin horar da su da ilimi da dabaru na zamani domin bunƙasa sanaoi sun a dogaro da kai a ko ina a Nijeriya.
Shi ma a jawabinsa wakilin gwamnan Kano kuma babban Darakta na hukuma mai kula da ƙananan masana’antu da matsakaita na jihar Kano DG Nasiru Mansur Muhammad ya ce ya tabbatar cewa wannan kamfani na Global Sight Serɓice Limited ya nemi gudunmawa ta gurin taro da kujerun zama da tsaro kuma gwamnatin Kano ƙarkashin shugabancin gwamna Abba Kabir Yusuf gwamnatin mai kishin jama’a ta ba su abinda suke buƙata domin bunƙasa ilimin masu wannan sana’a na Kano.
