Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Shugaban ƙaramar Hukumar Gwarzo Hon. Dakta Mani Tsoho Gwarzo, ya bayyana cewa ƙaramar Hukumar Gwarzo ta ƙara litattafan karatu da rubutu sama da dubu 10 domin rabawa ɗalibai na makarantu kamar yadda gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya tara shugabannin ƙananan hukumomi 44 na Kano da sakatarorin ilimi domin raba musu milliyoyin litattafai domin bunƙasa ilimi kamar yadda gwamnan ya yi alƙawari kuma yake cikawa akan ilimi da sauran fannoni na rayuwa da cigaban al’ummar Kano a wannan tafiya ta gwamnatin Kwankwasiyya ƙarƙashin jagorancin Madugun ta Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Haka kuma ya bayyana cewa yanzu haka kwalliya ta fara biyan kuɗin sabulu: “Mu a nan ƙaramar hukumar Gwarzo domin kuwa ɗaliban da suka karɓi waɗannan litattafai da gwamnatin Kano ta raba sun ƙara himma da ƙwazo wajen halartar makaranta cikin annashuwa da ƙarfin gwiwa wanda ya jawo ƙungiyar iyayen da malaman makaranta da sauran al’umma na bayyana farin cikinsu kan wannan aiki na bunƙasa ilimi a jihar Kano baki ɗaya.”
A ƙarshe Dakta Mani Tsoho Gwarzo shugaban ƙaramar hukumar Gwarzo kira ya yi da ma’aikatan ƙaramar hukumar da ɗaukacin al’ummar ƙaramar hukumar da ma Kano baki ɗaya da su cigaba da addu’a da haɗin kai da yabawa gwamna Abba da mataimakinsa Kwamarede Aminu Abdulsalam Gwarzo akan ayyuka da ake yi na bunƙasa noma, lafiya, hanyoyi, tsaro da dai sauransu a wannan gwamnati ta Kano.
