Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Dakarun Runduna ta 3 ta Sojojin Nijeriya da kuma dakarun ‘Operation SAFE HAVEN’ (OPSH) sun kashe ’yan bindiga uku a wani samame da suka kai da sanyin safiyar ranar 31 ga Mayu, 2025, biyo bayan samun bayanan sirri kan maɓoyar ’yan ta’adda da ke gefen ƙauyen Pinau a ƙaramar Hukumar Wase ta Jihar Filato.
A cewar wata sanarwar manema labarai da jami’in yaɗa labarai na rundunar ‘Operation SAFE HAVEN’ Manjo Samson Nantip Zhakom ya fitar, an kai harin ne kan wasu ’yan ta’adda da suka shahara wajen addabar al’umma da masu ababen hawa a kan hanyar Pinau zuwa Gimbi.
“Sojoji sun bi ‘yan ta’addan inda suka yi artabu da su, inda ƙarfin wuta na sojojin mu ya mamaye ‘yan bindigar, wanda ya kai ga kashe uku, yayin da wasu suka gudu da raunukan harbin bindiga,” inji sanarwar a wani ɓangare.
A jini a kan hanyoyin da suka tsere, wanda ya nuna cewa wasu da dama sun samu raunuka yayin arangamar. Binciken da aka yi a yankin ya kai ga gano bindiga ƙirar AK-47 guda ɗaya da kuma wata jakar alburusai, waɗanda a yanzu haka suke hannun sojoji domin ci gaba da bincike.
Manjo Zhakom ya ƙara da bayyana cewa, ana ci gaba da gudanar da ayyukan bin diddigin yadda za a kamo masu aikata laifukan da suka gudu da kuma tabbatar da ɗorewar zaman lafiya a cikin al’ummomin da abin ya shafa.
Ya tabbatar da ƙudurin sojojin na ci gaba da samun wannan nasarar, yana mai cewa, “Rundunar runduna ta 3/Operation SAFE HAVEN za ta ƙarfafa wannan nasarar da nufin ƙara ƙarfafa ayyukansu don ƙara ƙaimi wajen yaƙi da masu aikata laifuka a yankin.”
