Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kungiyar Kafofin Yaɗa Labarai Masu Zaman Kansu da Shirye-Shiryen Manufofi (IMPI) ta bayyana cewa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kawo gagarumin sauyi a tattalin arzikin Nijeriya ta hanyar aiwatar da manufofin ci gaba na tattalin arziki, wanda ya taimaka wajen fitar da ƙasar daga dogon zamani na almubazzaranci da rashin tsari.
A cikin wata sanarwar manufofi da Shugaban ƙungiyar, Dakta Omoniyi Akinsiju, ya rattaba hannu a kai, IMPI ta jaddada cewa wannan salo na gyaran tattalin arziki shi ne mafi dacewa wajen warware matsalolin da suka daɗe suna dabaibaye tsarin kuɗi da tafiyar da harkokin gwamnati a Nijeriya.
Sanarwar ta ce, kafin fara gyare-gyaren tattalin arziki a watan Mayun 2023, tsarin tattalin arzikin Nijeriya ya kasance ƙarƙashin tasirin wata ƙaramar ƙangiyar masu faɗa a ji da ta ƙunshi ‘yan siyasa, tsoffin jami’an soja da attajirai, waɗanda ke sarrafa manyan albarkatun ƙasa ta hanyar tsarin gata da rabon arziki na musamman, musamman a ɓangaren man fetur.
IMPI ta bayyana cewa tsarin tallafin mai ya zama wata hanya da wasu ke anfani da ita wajen amfana da dukiyar jama’a, inda aka daɗe ana zarginsa da cin hanci da almundahana. Haka kuma, kasancewar farashin musayar kuɗi da yawa ya bai wa wasu damar cin moriyar banbancin farashi tsakanin kasuwar hukuma da ta bayan fage, lamarin da ya janyo asarar kuɗaɗen gwamnati.
A cewar ƙungiyar, lokacin da Shugaba Tinubu ya karɓi mulki, kusan kashi 97 cikin 100 na duk kuɗaɗen shiga na gwamnati ana kashe su ne wajen biyan basussuka, al’amari da ta bayyana a matsayin mai matuƙar hatsari ga makomar tattalin arzikin ƙasa.
IMPI ta lissafa wasu muhimman matakan da gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Tinubu ta ɗauka, ciki har da sake fasalin tsarin haraji da manufofin kasafin kuɗi, aiwatar da kashe kuɗaɗe domin tallafa wa marasa galihu, harajin dukiya da arziki, kare haƙƙin ma’aikata da masu hannun jari, gyaran manufofin kuɗi da tsarin banki, da kuma saka jari a manyan ayyukan more rayuwa.
ƙungiyar ta kuma yi nuni da cewa rabon kuɗaɗen shiga daga Asusun Raba Kuɗin Tarayya ya karu sosai a shekarar 2025, inda matakan gwamnati uku suka raba sama da naira tiriliyan 33.27 a cikin watanni goma sha ɗaya na farko, wanda ya kai ƙarin kashi 30 cikin 100 idan aka kwatanta da makamancin lokacin a 2024. Wannan ƙaruwa, a cewarta, ta samo asali ne daga cire tallafin mai da kuma gyaran farashin musayar kuɗi, wanda ya haifar da rabon kuɗi mafi girma ga jihohi da ƙananan hukumomi.
IMPI ta kammala da cewa tsarin ci gaba na tattalin arziki da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa ya fara haifar da ɗorewar daidaito a tsarin kuɗi, tare da gina tubalin da zai bai wa Nijeriya damar samun cikakkiyar kwanciyar hankali da bunƙasar tattalin arziƙi a nan gaba.
