Daga WAKILINMU
Kungiyar Manoma ta ƙasa, wato AFAN, ta roƙi Gwamnatin Tarayya da ta yi ƙoƙarin rage kuɗin kayan aikin gona domin manoman ƙasar nan su samu damar bunƙasa sana’ar noma cikin nasara.
Shugaban ƙungiyar, Alhaji Muhammad Magaji Gettado, shi ne ya yi wannan roƙo yayin da yake zantawa da manema labarai, inda ya bayyana cewa idan aka samar da rangwamen kayan aikin gona kamar taki da iri da kuma magungunan feshi, babu shakka noma zai kara bunƙasa a Nijeriya.
Ya ce idan kayan aikin gona sun zama masu sauki, manoma za su ƙara ƙarfin gwiwar faɗaɗa ayyukansu na noma, musamman noma na rani da na damina. A cewarsa, hakan zai taimaka matuƙa wajen ƙara samar da abinci a cikin gida, da kuma kayan da za a sarrafa a masana’antu ko a fitar da su zuwa ƙasashen ƙetare.
Haka kuma, shugaban ƙungiyar, Muhammad Magaji Gettado, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi da su fara sayen rarar amfanin gona kai tsaye daga hannun manoma domin tanadin abinci, tare da sayar da shi ga al’umma a farashi mai sauki, kamar yadda ake yi a wasu lokuta a baya.
Muhammad Magaji Gettado ya kuma yi amfani da wannan dama wajen yabawa gwamnati mai ci bisa matakan da take ɗauka na bunƙasa noma a kasar nan ta hannun ma’aikatar gona ta tarayya da sauran hukumomi masu ruwa da tsaki a fannin noma.
