Daga USMAN KAROFI
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Paris Saint-Germain (PSG) ta sake lashe kofin gasar zakarun Turai ta UEFA bayan ta doke Arsenal a wasan ƙarshe da aka buga cikin tsananin fafatawa. Wasan ya ƙare da ci 1-1 bayan ƙarin lokaci, kafin PSG ta yi nasara a bugun daga kai sai mai tsaron gida domin kare kambunta.
Arsenal ce ta fara zura ƙwallo tun a minti na shida ta hannun Kai Havertz, lamarin da ya ba ta damar mamaye wasu sassan wasan. Sai dai PSG ta nuna jajircewa tare da dawowa cikin wasan, inda gwarzon ɗan wasanta Ousmane Dembélé ya rama ƙwallon daga bugun fenariti a minti na 65.
Bayan ƙarin lokaci ya kasa samar da wanda zai yi nasara, an koma bugun fenariti. A yayin bugun, duka ɓangarorin sun rasa wasu damar cin ƙwallo, amma kuskuren da Gabriel ya yi ya bai wa PSG damar lashe kofin. Nasarar ta ƙara tabbatar da matsayin PSG a matsayin ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin Turai masu ƙarfi a wannan zamani.
