Tsaro da abinci: Gwamnatin Tarayya za ta gyara da gina sabbin dam a faɗin ƙasar – Minista

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirinta na gyarawa tare da gina sabbin madatsun ruwa (dams) a sassa daban-daban na ƙasar domin ƙarfafa noma ta hanyar ban ruwa da kuma samar da wutar lantarki ta hanyar ruwa.

Ministan Ruwa da Tsabtace Muhalli, Farfesa Joseph Utsev, ne ya bayyana haka a ranar Laraba yayin da yake jagorantar Babban Sakataren Ma’aikatar, Mista Richard Pheelangwah, da wasu daraktoci na fasaha a ziyarar duba ayyukan Azare–Jere Irrigation Project da Gurara Multipurpose Dam a Jihar Kaduna.

Farfesa Utsev ya ce wannan shiri yana daga cikin muhimman ayyukan da Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya dora wa ma’aikatarsa, domin ƙara samar da abinci ta hanyar noma da ban ruwa, haɓaka samar da wutar lantarki, da kuma ƙirƙirar guraben aiki ga matasan ƙasar.

“Mun ziyarci waɗannan wurare ne domin tantance halin da ayyukan suke ciki, gano matsalolin da ake fuskanta, da kuma gano inda ake buƙatar gaggawar shiga tsakani.

Ya ƙara da cewa an riga an zaɓi wasu madatsun ruwa da za a gyara, sannan za a gina sabbi ciki har da waɗanda ke kan hanyar Sokoto–Badagry Highway domin ƙara yawan noman ban ruwa da kuma samar da karin wutar lantarki ga ƙasar.

A nasa ɓangaren, Manajan Ayyukan Azare–Jere Irrigation Project da Gurara Multipurpose Dam, Injiniya Gazali Tukur Mohammed, ya bayyana cewa matsalar rashin tsaro tana daga cikin manyan kalubale da ke hana aikin tafiya yadda ya kamata. 

Sai dai ya jaddada cewa tawagarsu na ci gaba da jajircewa wajen cika alƙawarin samar da ruwa ga Birnin Tarayya Abuja (FCT).

Ayyukan Gurara Multipurpose Dam da Azare–Jere Irrigation Project an samar da su ne ta Ma’aikatar Ruwa da Tsabtace Muhalli ta Tarayya, inda wasu sassan aikin aka ba kamfanin Grams and Abel ƙarƙashin tsarin haɗin gwiwar gwamnati da masu zaman kansu (Public–Private Partnership, PPP) domin kula da su da gudanarwa.

By ukarofi