Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bayyana cewa tsarin ƙarfafa jarin bankuna da ake aiwatarwa a yanzu ba kawai don bin ƙa’idar doka ba ne, amma wani mataki ne na dabarar ƙasa da nufin ƙarfafa tsarin kuɗi, tabbatar da juriya, da shirya bankunan ƙasar wajen taka muhimmiyar rawa wajen cimma burin tattalin arzikin Dala Yiriliyan ɗaya nan da shekarar 2030.
Mataimakin Gwamnan CBN mai kula da Tsarin Kuɗi, Philip Ikeazor, ne ya bayyana haka a Abeokuta, Jihar Ogun, yayin taron shekara-shekara na Association of Corporate Affairs Managers of Banks (ACAMB), inda ya ce wannan mataki “alama ce ta juriya da hangen nesa.”
Ya bayyana cewa manufar wannan shiri ita ce tabbatar da cewa bankunan Niieriya suna da isasshen ƙarfi don fuskantar girgizar tattalin arzikin duniya, faɗaɗa bayar da rance ga masana’antu da ɓangarorin tattalin arziki, tare da taka rawa wajen samar da ci gaba mai ɗorewa da fa’ida ga kowa.
A cewarsa, “Babban burin CBN a wannan shiri shi ne tabbatar da cewa bankunanmu suna da kariya mai ƙarfi daga girgizar tattalin arziki, suna ci gaba da tallafawa kasuwanci da masana’antu, kuma suna iya gogayya da sauran bankuna a duniya da ke fuskantar sauye-sauye marasa tabbas.”
Ikeazor ya ƙara da cewa shirin ya zo ne a wani lokaci da ake fama da tashin farashin kaya, sauyin ƙjmar musayar kuɗi, da kuma rashin daidaiton kasuwannin kuɗi a duniya, inda ya bayyana cewa manufar CBN ita ce ƙarfafa ƙarfi da ƙwarewar tsarin kuɗi na ƙasa.
Yayin da ya kwatanta wannan shirin da tsarin haɗa bankuna da aka yi a 2005 wanda ya canza fuskar tsarin bankuna a Nijeriya, Ikeazor ya ce wannan sabon shiri na da nufin ƙirƙirar manyan cibiyoyi masu ƙarfin jari waɗanda za su iya tallafawa ayyukan gina ababen more rayuwa, ƙarfafa ƙurƙire-ƙirƙire, da samar da ci gaba mai haca kowa.
“Wannan ƙarfafawa ba ƙarshen hanya ba ce, amma hanya ce ta cimma manufa — ta hanyar zurfafa tsarin bayar da rance, ƙara samun damar kuɗi, da goyon bayan tsarin bankin zamani na dijital,” inji shi.
Ya kuma yi kira ga shugabannin harkokin kuɗi da su kasance masu “jarumta da tsari” wajen taka rawa a sauya tattalin arzikin Nijeriya, yana mai tunatar da su cewa shekarar 2030 — wadda ita ce wa’adin cimma tattalin arzijin dala tiriliyan ɗaya — ta saura shekaru biyar kacal.
Shi ma shugaban ACAMB, Rasheed Bolarinwa, ya yaba da hangen nesan CBN, yana bayyana wannan tsarin a matsayin wata dama ta sake fasalin tsarin bankuna a Nijeriya bisa ginshiƙin amincewa, haɗin kai, da ci gaba mai ɗorewa.
Ya ce “Wannan shirin ba takunkumi ba ne, dama ce ta sake tunani game da yadda bankunan Nijeriya za su zama masu ƙarfi, amintattu, da haɗin gwiwa wajen tallafawa burin ƙasar na tattalin arzikin dala tiriliyan ɗaya.”
Bolarinwa ya jaddada cewa nasarar wannan shiri ba za ta auna da faɗaɗa ma’aunin jarin bankuna kaɗai ba, sai da ƙarfafa dangantaka tsakanin bankuna da abokan hulɗarsu — musamman ƙananan masana’antu, mata ‘yan kasuwa, da mutanen karkara da ba su da damar asusun banki.
