Alaafin na Oyo ya caccaki ƙasashen Yamma kan lalata al’adun Afirka

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMAMD

Alaafin na Oyo, Oba Abimbola Akeem Owoade, ya yi kira ga ƙasashen yammacin duniya da su daina yaɗa manufofi da koyarwa da suke saka ’yan Afrika su raina ko su watsar da gadon al’adunsu na gargajiya.

Alaafin ya yi wannan jawabi ne a ƙarshen mako yayin da yake karɓar tawagar ƙungiyar Al’adun Oyo a Wasashen Waje a garin Oyo, inda ya jaddada muhimmancin kare da girmama gadon al’adu na Afrika, musamman addinin gargajiya na Yarbawa.

Oba Owoade ya ce, an daɗe ana wulaƙanta addinin gargajiya na Afrika ta hanyar zargin shi da mugunta, har ma wasu daga cikin Afrikawa – musamman Yarbawa – suka fara guje wa sunayen iyayensu don karɓar sunaye da ba su da alaƙa da asalin su.

A cewarsa, “Addinin gargajiya wani ɓangare ne na gadonmu, kuma wajibi ne a kiyaye shi da mutuntawa. Barazanar da ke tunkarar wannan gado ta kai matakin da take lalata fahimtar ‘yan Afrika game da kansu.”

Ya ƙara da cewa, “Harin da ake kai wa addinin Yarbawa da tsarin zamantakewa da ruhaniya dole ne mu fuskance shi da cikakken ƙarfin imani da fahimta. Ni a matsayina na Alaafin, na ɗauki nauyin kare kowace rai ta Yarba, ko a nahiyar Afrika ko a ƙasashen waje.”

Oba Owoade ya bayyana cewa addinin gargajiya na Yarbawa na da darajar da ba za a iya auna ta ba, domin shi ne ke bayyana asalinsu, yana ba su fahimtar rayuwa, kuma yana haɗa su da kakanninsu don su sami hanyar da za ta kai ‘ya’yansu ga ci gaba da ɗaukaka.

A cewarsa, “A yau, tubalin addininmu na gargajiya yana fuskantar barazana daga wasu addinai da suka shigo Afrika. Hakan ya yi daidai da matsin tattalin arziki da manufofin ƙasashen waje suka haifar, wanda ke ci gaba da talauta ƙasashen Afrika.”

Oba Owoade ya bayyana cewa kowace al’ada tana da bayani kan yadda duniya ta samu halitta, inda ya ce, “A tsarin Yarbawa, ana ganin duniya ta ƙunshi duniyoyi biyu — ta zahiri da ta ruhaniya — kuma haɗin su ke samar da ƙarfin da ake kira Ase, wanda shi ne tushen rayuwa da iko a al’adarmu.”

Ya ƙara da cewa, “Addinin gargajiya na Yarbawa falsafa ce ta rayuwa kuma kimiyya ce ta halitta. Kuma a yau, an fi nazarin al’adun Yarbawa fiye da kowace al’adar Afirka, inda masana daga sassa daban-daban ke rubuce-rubuce da bincike a kai.”

Sarkin ya kuma bayyana cewa tsarin mulkin gargajiya na Yarbawa ya kasance mai tsari sosai tun zamanin da, yana da tsarin daidaitawa da kulawa, tare da girmama mata a matsayin masu tasiri a harkokin mulki — abin da ya nuna cewa tsarin mulkin Yarbawa ɗaya ne daga cikin tsofaffin nau’ukan dimokuraɗiyya a duniya.

By ukarofi