NLC ta buƙaci jami’o’i masu zaman kansu su shiga ƙungiyar ASUU

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC), Joe Ajaero, ya buƙaci jami’o’in masu zaman kansu a faɗin ƙasar nan da su shiga ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Nijeriya (ASUU), domin ƙarfafa yunƙurin ƙungiyar wajen inganta harkar ilimi a ƙasar.

Ajaero ya bayyana haka ne yayin wani taron tattaunawa na Toyin Falola Interview Series da aka gudanar a ranar Lahadi, mai taken “Tattaunawa da Shugaban ASUU, Farfesa Christopher Piwuna.”

Taron ya samu halartar masana da membobin al’umma daga sassa daban-daban na ilimi, inda aka tattauna kan matsalolin da ke addabar manyan makarantu a Nijeriya, ciki har da yawan yajin aikin ASUU, sakacin gwamnati, da kuma cin zarafin da ake yi wa mambobin ƙungiyar.

A yayin jawabin sa, Ajaero ya shawarci ASUU ta fara tattaunawa da jami’o’in masu zaman kansu kan yadda za a ƙunshi malamansu cikin ƙungiyar, yana mai cewa hakan zai ƙara ƙarfafa muryar malamai wajen neman haƙƙoƙinsu.

“Ya kamata a daina tsoratar da ASUU da mambobinta,” inji shi. “Abin mamaki ne yadda gwamnati ke sa hannu a yarjejeniya da ƙungiyar tun shekarar 2009 amma ta kasa cikawa.”

Ya kuma zargi gwamnati da cewa asalin dalilin kafa wasu ƙungiyoyin ilimi da kuma yawaitar jami’o’in masu zaman kansu shi ne domin raunana ƙungiyar NLC da raba haɗin kan malamai.

Ajaero ya kuma yi kira ga dukkan ƙungiyoyin jami’o’i da su haɗa kai su fito da matsaya guda wajen fuskantar gwamnati don neman cikakken gyaran tsarin ilimi.

A nasa ɓangaren, Shugaban ASUU, Farfesa Chris Piwuna, ya ce ainihin ikon cin gashin kai da nagartar jami’o’i ba za su tabbata ba sai idan gwamnati ta samar da kayan aiki da tallafi da suka dace ga malamai.

Ya ƙaryata zargin cewa ASUU tana son kai kawai, yana mai cewa mambobin ƙungiyar suna ci gaba da sadaukarwa duk da tsangwama daga hukumomi.

By ukarofi