Za mu ɗauki mataki kan jam’iyyun da ke haifar da rikici – INEC

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa ba za ta ci gaba da zama shiru ba yayin da rashin daidaito da rashin bin doka ke ci gaba da wanzuwa a cikin jam’iyyun siyasa.

Shugaban INEC, Farfesa Joash Ojo Amupitan, ya bayyana haka ne a Awka jim kaɗan bayan kammala zaɓen gwamnan Anambra wanda gwamna mai ci, Farfesa Charles Chukwuma Soludo, ya lashe.

Ya ce rashin dimokuraɗiyyar cikin gida a jam’iyyun siyasa da rikicin shugabanci suna matuƙar damun hukumar, domin suna lalata tsarin zaɓe kuma suna jawo asarar kuɗaɗe da lokaci.

Farfesa Amupitan ya bayyana cewa sama da kashi 75 cikin 100 na ƙarar kotu da ke shafar siyasa a ƙasar nan na da alaƙa da rikicin cikin gida a jam’iyyun siyasa da kuma zaɓen fidda gwani da aka gudanar ba bisa tanadin kundin tsarin jam’iyya ba.

“Duk lokacin da jam’iyya ta je kotu, dole ta haɗa da INEC a shari’a, wanda hakan ke sa mu ɗauki lauyoyi, mu biya su kuɗi, kuma ba ƙaramin kashe kuɗi ake yi ba,” inji shi.

Ya ƙara da cewa, INEC na da ikon doka wajen sa ido da kula da ayyukan jam’iyyun siyasa, amma wasu lokuta ana ƙoƙarin rage wannan iko, abin da ya ce yana da haɗari ga dimokuraɗiyyar ƙasa.

Amupitan ya ce, hukumar za ta ƙarfafa tsarin sa ido a kan jam’iyyun domin tabbatar da cewa suna bin ƙa’idojin da doka ta tanada, tare da tabbatar da cewa ba a sake maimaita irin matsalolin da ake gani ba.

Farfesa Amupitan ya nuna damuwa kan yadda ake samun sabani a tsakanin kotuna masu daidaiton matsayi — musamman a lokutan da jam’iyya ɗaya ke samun umarni daban-daban daga kotuna biyu.

“Misali, yanzu wani kotun tarayya a Abuja ya ce PDP kada ta gudanar da babban taro, amma wani kotu daga Ibadan ya ce sai ta gudanar da taron. Wannan irin ruɗani ne ke haifar da rashin kwanciyar hankali a siyasa,” inji shi.

Ya ƙara da cewa, hukumar zaɓe ba za ta lamunci irin wannan ruɗani ba, kuma za a ɗauki mataki akan duk jam’iyyun da suka ci gaba da aikata irin waɗannan abubuwa.

Dangane da batun ƙirƙirar kotuna na musamman da za su riƙa gudanar da shari’o’in zaɓe, Amupitan ya ce ba zai yiwu hakan yanzu ba sai an yi wa kundin tsarin mulki gyara.

Sai dai ya bayyana cewa kotunan zaɓe da ake da su yanzu — waɗanda suke ƙarƙashin kundin tsarin mulki — su ma kotuna na musamman ne, domin ana kafa su ne musamman don sauraron ƙarar zaɓe.

“Misali, idan kotun ɗaukaka ƙara ke zama a matsayin kotun zaɓen shugaban ƙasa, to a wannan lokaci tana zama kotu ta musamman. Saboda haka muna da kotunan da suka dace, sai dai ana tattaunawa kan yadda za a rage lokaci da taƙaddama wajen yanke hukunci,” inji shi.

By ukarofi