Tsoffin shugabannin Nijeriya na dakon wanda maye gurbin Tinubu a 2027

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A wani rahoto da jaridar Platinumpostng ta yi, ya nuna cewa, a wani yunƙuri na tunkuɗe shugaban ƙasa Bola Tinubu gabanin zaɓen 2027, tsoffin shugabannin Nijeriya uku, Olusegun Obasanjo, Ibrahim Babangida, Abdulsalam Abubakar da manyan hafsoshin soja sun fara neman tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya zo a ceto ƙasar.

Har ila yau, a ganawar sirrin da suka yi a Minna a ƙarshen makon da ya gabata, akwai ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP zaɓen 2023, Peter Obi.

Manyan hafsoshin yaƙin basasar Nijeriya da ke nuna damuwa kan rugujewar jam’iyyar adawa ta PDP sun ƙaddamar da farmaki kan tsohon gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike da abokansa domin ceto jam’iyyar daga rugujewa.

Platinum Post ta ruwaito cewa, tsofaffin shugabanni uku masu faɗa a ji kuma tsohon mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Janar Aliyu Gusau (mai ritaya) sun gana a Minna babban birnin jihar Neja a kwanan baya don tsara yadda za su karɓe jam’iyyar.

Kamar yadda wata majiya mai tushe ta bayyana cikakken bayanin taron, taron manyan hafsoshin sojan da suka yi ritaya na da manyan ajanda biyu da suka haɗa da ceto tsarin jam’iyyar daga hannun Wike da kuma neman wanda ya dace da shugaban ƙasa wanda zai kayar da shugaba mai ci Bola Ahmed Tinubu.

Majiyar ta bayyana cewa manyan hafsoshin sojan da suka yi ritaya sun damu da yadda al’amuran jam’iyyar PDP ke fuskantar kasadar rugujewa, inda suka yanke shawarar haɗuwa da juna da nufin tsara hanyar da za a bi domin samun ci gaban jam’iyyar.

Tsoffin shugabannin mulkin sojan da aka ce ba su gamsu da salon mulkin shugaba Tinubu ba, tuni suka fara dakon ɗan takarar shugaban aasa mai sahihanci gabanin zaɓen 2027.

Idan dai za a iya tunawa, ‘yan jam’iyyar IBB da Obasanjo da Ali Gusau su uku ne suka jagoranci kafa jam’iyyar PDP a shekarar 1998.

Don haka, sun tuntuɓi tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark da nufin karɓar shugabancin jam’iyyar PDP daga Umaru Iliya Damagun wanda abokin Ministan babban birnin tarayya ne.

Platinum Post ta tattaro cewa, lokacin da aka fara tuntuɓar David Mark wanda ke hutu a Amurka, ya ƙi amincewa da aikin na ceto PDP daga nuste a ruwa.

An haifi tsohon shugaban majalisar dattawa kuma gwamnan jihar Neja na mulkin soja a jihar Benuwai a ƙarshe ya amince da buƙatar Janar Babangida da ake yi wa laƙabi da ubangidansa kuma mai taimakonsa.

Majiyar ta jaddada cewa, “Janar-Janar ɗin a taron Minna suna son Mark ya kasance mai jan ragamar al’amuran jam’iyyar PDP yayin da suke dakon ɗan takarar shugaban ƙasa na gaskiya wanda zai kayar da Tinubu a 2027,” inji majiyar.