Fubara zai gina asibitin mahaukata a garin su Wike, ya ce za su buƙace shi ba ​jimawa ba

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara ya amince da gina asibitin masu taɓin hankali na zamani a ƙaramar hukumar Obio-Akpor, garin tsohon mai gidansa a harkokin siyasa, Nyesom Wike, Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja. 

Wannan matakin dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun takun saƙa tsakanin jiga-jigan ‘yan siyasan biyu, waɗanda suka yi ta samun saɓani a kan mulkin Jihar Ribas.

Wike, wanda ya fito daga yankin Rumuepirikom a Obio-Akpor, ya fito fili ya soki Fubara, inda ya zarge shi da cin amanar waɗanda suka taimaka masa ya hau mulki.

A wani liyafar da ‘yan ƙabilar Ijaw suka shirya a garin Fatakwal, Wike cikin kwarin gwiwar ya ce a ƙarshe zai koya wa Fubara da magoya bayansa darasi, inda ya ce, “Kuɗi ba ya cin nasara a siyasa. Idan lokaci ya yi, za mu yi siyasa, mu koya musu ainihin abin da take nufi.”

A martanin da ya mayar, yayin wani taron coci da aka gudanar a cocin St. Paul’s Cathedral a wani ɓangare na bikin murnar zagayowar ranar samun ‘yancin kan Nijeriya karo na 64, Fubara ya kare ayyukan gwamnatinsa, inda ya kwatanta shi da nasarorin da gwamnatin da ta gabata ta samu. 

Ya bayyana muhimman ayyukan samar da ababen more rayuwa da suka haɗa da titin zobe na Fatakwal da titin Trans-Kalabari, a matsayin shaida na ingancin gwamnatinsa, yana mai cewa waɗannan sun zarce abin da gwamnatin Wike ta samu cikin shekaru takwas.

Fubara ya kai wa abokan hamayyar siyasarsa jab kai tsaye ta hanyar yi masa ishara da asibitin masu taɓin hankali a yankinsa na Obio-Akpor, yana mai cewa, “Na gina asibitin masu taɓin hankali a babban asibitin da muke ginawa saboda za su buƙaci hakan nan ba da daɗewa ba.”

Ya ci gaba da tabbatar da cewa nasarorin da ya samu na shekara guda sun mamaye aikin da aka yi a lokacin mulkin Wike, yana mai kiran abokan hamayyarsa “kwantena marasa amfani suna hayaniya.”

Gwamnan ya kuma jaddada cewa ayyukan gwamnatin sa na amfanin al’ummar jihar Ribas ne, ba wai don kasuwanci na kashin kai ba. Ya jaddada cewa manufofinsa sun fi mayar da hankali ne kan ci gaba mai ma’ana, ba wai “aikin a gani” na bukukuwan ƙaddamar da ƙasa ba. “Duk abin da nake yi, ina yi wa mutanen jihar Ribas ne,” inji Fubara, inda ya yi alƙawarin cewa za a kammala dukkan ayyukan da aka fara a ƙarƙashin gwamnatinsa tare da amfani da jama’a.

Ya kuma bayyana kwarin gwiwar cewa duk da ƙalubalen da yake cigaba da fuskanta daga masu sukarsa, gwamnatinsa za ta ci gaba da aiwatar da manufofinta na ci gaban jihar, bisa himma wajen kare muradun jihar.

By ukarofi