Tsohon ɗan wasan Arsenal Aubameyang ya tsallake rijiya da baya a hatsarin mota

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wani babban hatsarin mota ya rutsa da tsohon ɗan wasan gaba na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal, Pierre-Emerick Aubameyang a lokacin da yake kan hanyar zuwa atisaye a ranar Alhamis, 26 ga Nuwamba, 2026.

Ɗan ƙasar Gabon ɗin, wanda a halin yanzu yake buga wa ƙungiyar Deportivo La Coruña ta ƙasar Sifaniya, ya haɗu da iftila’in ne a lokacin da motar da yake ciki ta yi kiciɓis da wata mota yayin da yake kan hanyar tafiya zuwa filin atisayen ƙungiyar tasa. Duk da wannan hatsari, Aubameyang ya samu zuwa wajen karɓar horon kamar yadda aka tsara.

Ɗan wasan mai shekaru 37 daga bisani ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata wallafa da ya yi a shafinsa na Instagram, yana mai tabbatar wa magoya baya cewa babu wanda samu rauni a sakamakon faruwar hatsarin duk da cewa ya ce ya shiga halin firgici a lokacin.

A baya dai Aubameyang ya buga wa ƙungiyoyin Arsenal da Barcelona a Nahiyar Turai. Al’amarin ya auku ne yayin da Deportivo ke shirin karawa da Barcelona a gasar Laliga a ƙarshen makon nan.

By Babaji

Leave a Reply