Tsohon Gwamnan Yobe, Bukar Abba Ibrahim ya kwanta dama

Daga BASHIR ISAH

Tsohon Gwamnan Jihar Yobe, Bukar Abba Ibrahim, ya rasu a daidai lokacin da yake jinya a wani asibitin Kasar Saudiyya.

Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ne ya tabbatar da rasuwar marigayin cikin sanarwar da ya fitar ta bakin Darakta Janar na Yada Labarai ga Gwamnan, Mamman Mohammed.

Sanarwar ta ce a ranar Lahadi marigayin ya cika, kuma a Saudiyya za a binne shi.

Ana sa ran Gwamna Mai Mala Buni ya yi zaman karbar ta’aziyyar rasuwar a Fadar Gwamnatin Jihar da ke Damaturu.

Abba Ibrahim ya bar duniya yana da shekara 75, kuma shi ne miji ga ‘yar majalisa Khadija Bukar Abba Ibrahim, mai wakiltar Gujba, Gulani, Damaturu da Tarmuwa a Majalisar Tarayya.