Zuwa ga al’ummar Arewa

Spread the love

Assalamu alaikum.

Bayan gaisuwa mai tarin yawa tare da fatan alheri gare ku duka, ina kuma mai jajanta muka akan halin da muka tsincin kanmu a yau.

Ina fatan wannan wasikar tawa ta same ku lafiya, cikin koshin lafiya da walwala.

Na rubutu muku wannan wasikar ne domin na isar muku da sakona tare da fatana gare ku. Ina mai shaida muku cewa, kaunarku ce ta sa na rubutu wannan wasikar, domin masu iya magana kan ce ‘Idan kunne ya ji…’ Wannan wasiqar ita ce babbar gudunmawar da zan iya bayarwa a halin yanzu, bayan koyar da yara da nake a makaranta. Duk wata gudunmawa da zan bayar, ba ta kaita ba, don koyarwa ta fi ko wace irin gudunmawa. Domin kalamun da ke cikinta za su fi mana amfani a irin halin da muka tsincin kanmu A yau.

Kamar yadda muka sani A yau cewa, Duk wasu jihohin Arewa babu kwanciyar hankali, jihohin Borno da Katsina da Zamfara da Kaduna da Taraba da Yobe sun zama tamkar sansanin ‘yan ta’adda, kullum a cikin zullumi da kisan kiyashi ake yi wa al’umma kai kace babu gwamnati a kasar.

Abu mafi muhimmanci da ya kamata mu mai da hankali a kai shi ne, neman ilimin addini da na boko. Amma fa mu sani, karatun addini shi ne ya zamo mai gudanar da rayuwarmu, ba na boko ba. Da yawan ‘yan boko A yau sun watsar da addini sun bi kafirai sun kafirce wa Allah da Annabinsa, sun bijire musu, sun yi watsi da umarninsu, shi ya sa ma ake hada baki da wasunsu ake zaluntar mu.

Neman ilimi abu ne mai muhimmanci, domin babu wata kasa da ta ci gaba a duniya alhali tana yi wa ilimi riqon sakainar kashi. Dole mu farga! Mu dawo cikin hayyacinsu, mu dawo daga rakiyar mutanen da basa kaunarmu, basa son ci gabanmu.

Mu zama musu dogaro da kai, ta hanyar kirkirowa kanmu hanyoyin samun mafita na rayuwa. Wannan zai taimaka wajen fitar da Arewa daga halin da take ciki a yau. Babu wani dalili da zai sa mu zauna muna kiran babu aikin yi, alhalin Allah ya yi mana baiwa da hikimar dogaro da kai.

Matasanmu a yau ba sa son motsa jiki, kowa sai jiran ganima daga gwamnati, wanda wannan kuma babban kuskure ne. Allah bai ce kowane dan boko sai ya zama ma’aikacin gwamnati ba, kuma bai ce kowane ma’aikacin gwamnati sai ya zama mai kudi ba. Amma idan muka tsaya da kafarmu muka jajirce, Allah zai bamu mafita.

Kar mu dauka da zarar sun kammala karatun boko mun gama samun komai na rayuwar duniya. Lallai karatun boko abu ne mai kyau, domin zai haska mana hanyar da ya kamata mu bi ta fuskar ilimi, amma ba abin dogaro ba ne wajen neman duniya da rufin asiri, domin akwai wadanda Allah ya yi wa arziki a yau, amma ko ajin firamare ba su taba shiga ba.

Zancen mutum ya zauna yana tunanin aikin gwamnati wannan ya kau, ya kamata mu zamo masu kwazo da himma wajen dogaro da kai, domin mafi yawancin abin da ke cutar da mu a yau ke nan, ragganci da sun ci a kwance, don mun ga wani ya daukaka sai suce tilas sai mun zama tamkar shi, wanda idan aka yi rashin sa’a, sai mutum ya tsinci kansa a wani mugun yanayi wanda kan jefa al’umma cikin fargaba da tashin hankali.

Wannan ne kadai hanyoyin da ya kamata mu bi wajen kau da dukkan ‘yan ta’adda da ta’addanci a Arewa, saboda an rabamu da Ubangiji, kuma ana amfani da ‘ya’yanmu wajen rusa mu.

Da wannan na kawo karshen wannan wasikar tawa. Ina rokon Ubangiji Allah ya yi mana jagora, ya taimake mu a dukkan lamuranmu, kuma ya sa Arewa ta ci gaba da zama lafiya.

Wassalam.

Daga Muhammad Auwal Musa (Ya Muha). 08062327373

By Editor