NYSC ta daina tura masu yi wa ƙasa hidima zuwa jihohi masu fama da matsalar tsaro – Gwamnati

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa, ta daina tura masu yi wa kasa hidima (NYSC) zuwa jihohin da ke fama da matsalar tsaro a fadin kasa.

Rahotanni sun ce masu yi wa kasa hidima da dama ne aka yi garkuwa da su yayin da aka tura su sassan kasa domin hidimta wa kasa na shekara guda bayan kammala karatu.

An jiwo Ministar Harkokin Matasa, Jamila Ibrahim na cewa, gwamnati ta dauki sahihan matakai domin bai wa masu yi wa kasar hidima kariya ciki har da daina tura su zuwa yankunan da ke fama da matsalar tsaro.

A cewarta, “A matsayin matakin nan take daga bangaren gwamnati da hukumar NYSC, mun dakatar da tura masu yi wa kasa hidima zuwa jihohin da ke fama da matsalar tsaro.”

Jamila ta bayyana haka ne a wani shiri da tashar Channels Television ta yi da ita a ranar Lahadi.

Ta kara da cewa, “Mun saba yin hakan a baya. Akwai jihohin da ba mu tura masu yi wa kasa hidima don tabbatar da ba su kariya.”

Kazalika, ta ce akwai bukatar masu bai wa ‘yan hidimar kasa tsaro su hada kai da sauran hukumomin gwamnati wajen yin aiki tare.

Saboda a cewarta, “Idan ana batun tsaro, abu ne da ya shafi bangarori da dama. Don haka aikin ba na NYSC kadai ba ne da Ma’aikatar da take karkashinta.

“Muna aiki da hukumomin tsaro don tabbatar da kariyar ‘yan hidimar kasa.”

By Editor