Aure mai nagarta maganin nadama

Spread the love

Aure abu ne wanda ya wuce a yi wasa da shi, don haka ni ke son amfani da wannan dama in kawo ‘yar shawara ga ‘yan uwa na talakawa. Duk auren da aka gina bisa cencenta ya kuvuta daga tozarta don haka sai mun yi karatu a natse mu gano bakin zaren.

Kana talaka tikif amma a kullum gurin ka wanda zai zo neman auren ‘yarka daga mawadaci sai mai wata daukaka, ka manta cewa tun a zamanin baya ma su wadata kadan ne ke zuwa su auri ‘yar talakawa ina ga yanzu da zamani ya zamo na idan ba kai ba ni wuri. Jama’a mu na dai ji da ganin yadda mutane ma su manyan mukamai ke bani in baka a tsakanin zurriyar su.

Hakan ne alamta ma talakka cewa kwarya ta bi kwarya. Ban ce ba a auratayya a tsakanin mawadata da talakkawa ba, amma a takaita dogon hange na son abun duniya ‘yar ku amana ce isar ta aure hakki ne wanda ya rataya a kanku idan har kun sauke kun yi abinda ya dace idan kuma an tsaya sai wanda ake bukata a karshe ai nadama.

Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa. 07066434519.

By Editor