Tsadar rayuwa ta haifar da zanga-zanga a Neja

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Al’ummar garin Minna, babban birnin Jihar Neja, sun gudanar da zanga-zangar lumana domin nuna rashin jin dadinsu dangane da tsadar rayuwar da ake ci gaba da fuskanta a Nijeriya.

An ga masu zanga-zangar a ranar Litinin sun mamaye wasu manyan hanyoyin garin wanda hakan ya haifar da tsaikon zirga-zirgar abubuwan hawa.

MANHAJA ta kalato cewar, mazauna yinkin Kpakungu da ke Minna sun yi cincirindo a kan hanya daidai randabawul da ke yankin inda suka hana masu abubuwa hawa shiga da fita.

Bayanai sun ce jama’ar sun bukaci ‘yan sandan da suka bayyana a wurin don kula da dandazon da su hanzarta barin wurin ko kuma su gamu da fushin jama’a.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun daga kwalaye masu dauke da sakonni daban-daban kamar “Babu Abinci, muna mutuwa saboda yunwa” da dai sauransu.

Masu zanga-zangar sun kuma zargi masu rike da mukaman siyasa a jihar da rashin adalci wanda a cewarsu hakan ne ya jefa al’umma cikin halin kunci.

By Editor