Tunawa da shekaru 49 da kisan Janar Murtala Ramat Muhammed 

Daga TASKAR NASABA

A ranar 13 ga Fabrairu, 1976, aka kashe shugaba mulkin soja na Tarayyar Nijeriya, Janar Murtala Ramat Muhammed, a wani yunƙurin aikata juyin mulki da bai yi nasara ba.

An kuma kashe direbansa da gwamnan mulkin soja na Jihar Kwara, Kanar Ibrahim Taiwo a lokacin.

Yunƙurin juyin mulkin Nijeriya a shekarar 1976, wani yunƙuri ne na juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijeriya a ranar 13 ga Fabrairu, 1976, a lokacin da wani ɓangare na hafsoshin sojin ƙasar ƙarƙashin jagorancin Laftanar Kanar Bukar Suka Dimka suka yi yunƙurin kifar da Gwamnatin Janar Murtala Ramat Muhammed (wanda ya karɓi mulki a juyin mulkin 1975).

An kashe Janar Murtala a Legas (tsohon Babban Birnin Tarayyar Nijeriya a lokacin) tare da dogarinsa, Laftanar Akintunde Akinsehinwa, a lokacin da wasu sojoji ƙarƙashin Dimka suka yi wa motarsa ​​kwanton-ɓauna a Ikoyi kan hanyar zuwa Dodan Barrack. 

A cikin shirye-shiryen rediyo da aka watsa ga al’ummar ƙasar, Dimka ya ambaci cin hanci da rashawa, yanke hukunci, kamawa da tsarewa ba tare da shari’a ba, da rauni daga ɓangaren Gwamnatin Murtala da rashin iya gudanar da Mulki a matsayin dalilan kifar da Gwamnati.

Sojojin Gwamnati masu biyayya ga Gwamnati sun murƙushe yunƙurin Juyin Mulkin bayan sa’o’i da dama.

Bayan farautar makwanni uku, ana neman Dimka, daga bisani an kama Dimka a kusa da Abakaliki a Kudu maso Gabashin Nijeriya a Ranar shida ga watan Maris 1976.

Laftanar Janar Olusegun Obasanjo ne ya gaji Janar Murtala Muhammed a matsayin Shugaban Ƙasa.

Mulkin Obasanjo tare da maƙarranbansa a Gwamnati, da suka haɗa da; Shehu Musa Yar’adua, da TY ɗanjuma, da Ibrahim Badamasi Babangida, da Domkat Bali, sun yi ƙoƙarin ganin sun aiwatar da ayyukan da Murtala ya ƙudurta gudanarwa a Nijeriya.

Saboda kimar Janar Murtala Muhammed ne a Nijeriya, aka sanya hotonsa cikin Kakin Soji a kuɗin ƙasar, Naira 20.