Turji na barazanar kashe mutanen da ya yi garkuwa da su bayan sojoji sun kama na hannun damansa

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Ƙasurgumin ɗan bindiga Bello Turji ya sha alwashin kashe mutanen da yake garkuwa da su a halin yanzu, matuƙar gwamnatin Najeriya bata saki abokin ta’addancinsa ba wato Baƙo Wurgi.

Blueprint Manhaja ta rawaito cewa rundunar sojin Najeriya ta ɗaya ta cafke ƙasurgumin ɗan bindiga mai suna Baƙo Wurgi a Jihar Zamfara.

Ana zargin Wurgi da hannu a kisan Sarkin Gobir na Sabon Birni a Jihar Sakkwato, Alhaji Isa Mohammed Bawa.

Rahotanni sun bayyana cewa ƙasurgumin ɗan bindiga, Bello Turji, tuni ya fara tuntuɓar dagatai da ke Shinkafi a Jihar Zamfara, inda ya yi barazanar kai wa al’umominsu hari muddun ba su sa baki ba wajen ganin an saki abokinsa Baƙo Wurgi wanda ke tsare a hannun jami’an tsaro.

Wasu majiyoyi da ke da masaniya kan lamarin sun bayyana cewa, Turji ya gargaɗi masu faɗa a ji da suka haɗa da sarakunan gargajiya, majiyar ta ce, “Tuni ya tuntuɓi masu faɗa a ji a yankin Shinkafi kamar dagatai da masu unguwanni, inda ya yi barazanar kai hari ga al’ummarsu don ganin sun taimaka wajen sakin Wurgi.

“Turji dai ya yi alƙawarin yin duk mai yiwuwa don ganin an sako Wurgi.” kamar yadda Zagazola Makama mai bincike kan aikace aikacen ‘yan ta’adda ya bayyana.

Majiyarmu ta cigaba da cewa, Turji ya sha alwashin ƙara ta’azzara lamarin rashin tsaro a yankin idan haƙarsa bata cimma ruwa ba.

“Ya sha alwashin kashe wasu daga cikin waɗanda yake garkuwa da su a halin yanzu, waɗanda suka haɗa da mazauna garin Isa, Sabon Birni da Shinkafi,” in ji majiyar.

Wannan dai ba shi bane karon farko da Turji ke yin irin wannan barazana ba ga hukumoni, don su saki wani daga cikin kwamandojinsa da aka kama.

Rahotanni sun bayyana cewa shekaru biyar da suka gabata, Turji ya taɓa yi wa hukumomi irin wannan barazanar wadda ta tilasta wa gwamnati sakin Dikko Chida, wani kwamandan Turji.

A lokacin, Turji ya yi barazana ga jami’an tsaro da hukumoni da suka kama Chida, game da sakinsa wanda a ƙarshe ya haifar da tattaunawar sakin ɗan bindiga Chida.

By ukarofi