Gwamnan Zamfara ya ƙaddamar da aikin titi a Ribas da yaba wa Gwamna Fubara

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jinjina wa Gwamna Siminalayi Fubara kan ƙoƙarinsa na samar da ayyukan ci-gaba a Jihar Ribas.

Kasancewar sa babban baƙo a yayin buɗe ayyukan titin Opobo da gadoji a ƙaramar hukumar Opobo/Nkoro a ranar Litinin, Gwamna Lawal ya yaba da hoɓɓasa da gwamnan na Ribas ke yi wa al’ummar jihar.

Ya kuma yaba da ayyukan inganta harkokin tattalin arziƙi don amfanar da al’ummar jihar.

Cikin wata takarda da Kakakin Gwamna Lawal, Sulaiman Bala Idris ya fitar, gwamnan ya ce samar da titina za su taimaka wa harkokin kasuwanci da faɗaɗa damammaki ga yankunan dake wajen jihar.

Ya kuma ce ayyukan da Fubara ke yi sun dace da irin ƙoƙarin da ya ke yi wa al’ummar jiharsa ta Zamfara wajen bunƙasa hanyoyi tattalin arziƙi da wasu manyan gyare-gyare da gwamnatinsa ke yi a jihar.

A nasa jawabin, Gwamna Fubara ya yi godiya ga Gwamna Lawal bisa amsa gayyatar da ya yi masa na buɗe ayyukan masu muhimmanci.

By Babaji