
Daga BELLO A. BABAJI
Ɗan wasan Super Eagles, Ademola Lukman ya lashe kyautar CAF ta shekarar 2024.
An gudanar da taron bada lambobin yabon ne a ranar Litinin, a birnin Marrakech na ƙasar Morocco.
Lukman ya nuna bajinta matuƙa wa ƙungiyarsa ta Atalanta dake ƙasar Italiya a kakar Bara inda ya taimaka mata ta lashe kofin gasar Europa. A wasan ƙarshe ne ya zura ƙwallaye uku a raga.
Ya kuma taka rawar gani wa Super Eagles a gasar kofin ƙasashen Afirka, wato AFCON ta 2024.
