
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnatin Tarayya ta sanar da sauya sunan Jami’ar Abuja (UniAbuja) zuwa Jami’ar Yakubu Gowon (Yakubu Gowon University).
Ministan Labarai, Mohammed Idris ya bayyana hakan ga manema labarai na Fadar shugaban ƙasa bayan zaman Majalisar Zartarwa (FEC) da aka gudanar ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu, a ranar Litinin.
An ƙaddamar da hakan ne don karrama tsohon shugaban mulkin soji na Nijeriya, Janar Yakubu Gowon mai ritaya, wanda a kwanan nan ne ya yi bikin cika shekaru 90 a duniya.
Ministan ya ce za su miƙa buƙatar sauya sunan ga Majalisa domin tabbatarwa.
Da farko, Blueprint ta ruwaito cewa FEC ta amince da jigilar matafiya ta jiragen ƙasa a kyauta yayin bukukuwan ƙarshen shekara.
