MAKAMASHI: Waiwaye adon tafiya

Spread the love

Tare da BASHIR MUDI YAKASAI 

Masu hikima na cewa, “waiwaye adon tafiya”, hakan ya biyo bayan rashin wutar Lantarki na tsawon kwanki kusan goma sha daya a dukkan arewacin Nigeria. Zantuka ta ko ina kamar ruwan dare daga bakuna daban-daban, wasu masu ma’an, wasu ban haushi, wasu kuma masu ban dariya, kuma shifcin gizo tattare da wawta da jahilci.

Wannan ya sa muka yanke shawara da mu yi waiwaye duk da cewa, a wannan fili mun taɓa  ambatawa,  mene ne makamashi? Yaya tarihin makamashi ya ke a wannan ƙasa ta Nijeriya? Tarihin ya nuna cewa, ƙasar Kano ce, ƙasar farko a duk faɗin ƙasashen Hausa, Katsina  da Daura da Rano da Zazzau, wato Zariya da Gobir da kuma ƙasar Gwandu da ta fara samar da makamashi da ake kira “KARMO”

Karmo ya ƙunshi itacen yakuwa da itacen lalle da itacen kuɓewa da itacen auduga da itacen tafasa, sai kuma kashi na biyu na makamashi shi ake kira da ‘kara zube’, wato karan dawa, wanda bayan girbi da kaka ba a kwashe shi an yi bishiyar a gona  ba, yana barbaje a gonaki shi yara ’yan makaranta da suka je daji samo makamashi suke kira ‘kara zube’.

Saboda haka tun shekara ta 1616 Miladiya shekaru 408 kenan yara ’yan makarantar allo a Kano suka zo da wannan fasaha ta amfani da karmo da kara zube a matsayin makamashi ga wannan daular ta ƙasar Hausa. Amma fa sarrafa wuta, kimiyar da fasahar ba sabon abu ba ne a arewacin Najeriya saboda ƙwarewarsu, kajen sarrafa ƙarafa iri-iri.

A arewacin Najeriya akwai sassa huɗu, waɗanda suke sarrafa ƙarafa kamar tama da tagulla da kuma kuza da azurfa da kuma zinariya ta amfani da makamashin gawayin itacen ƙirya bayan sun haɗa masa wuta ta amfani da zuga-zugan fata nan don nan za ka ga wuta har launin shuɗi take, don ruruwa. Haka ya na faruwa a Naraguta kusa da Jos a yankin Jihar Filato da Dutsen Dala da Gaya a Jihar Kano da Taruga a kusa da Abuja duka shekaru 3,500 kafin haihuwar Annabi Isah (S.A).

Allah mai zamani zuwan Turawan da tsare-tsaren sun na mulkin mallaka suka daƙile dukkan wata fasaha da kimiyya da muka bijiro da ita da tasu, farko ita ce ta makamashin kwal da ake haƙowa daga Inugu da Binuwai da Nassarawa da Abuja da kuma Jihar FIlato, hakan ya biyo bayan haɗe kudancin da Arewacin wannan ƙasa a shekara ta 1914 suka raɗa mana suna Nigeria.

A shekara ta 1922 bayan sun tabbata mulkin mallaka ya kankama a ko’ina suka kakkafa dokoki da tsare-tsare na rusa duk wata kafa ta cigaba (deɓelopment) na farko a sha’anin ilimi na kimiyya da fasaha suka soke shi cikin hikima suka mayar da shi ilimin dillanci, wato dillancin al’adu da ɗabi’u da halaye na Bature kuma munanan musamman sata da cin hanci da rashawa da kuma son kai, sai mutum ya kare da zama ɗan takarda (elite), wato jaki da kayan littattafai.

Saboda haka za ka ga a najeriya dakta da farfesa a sha’anin kimiyya da fasahar injiyan ƙarafa da ma’adanai da tattalin arziki da siyasa da sha’anin mulkin jama’a da zamantakewa, kai da dukkan fannoni na rayuwa ba sai iya ɗora taku ɗaya abu da iyaye da kakanni suka zo da shi shekaru dubbai kafin zuwan waɗannan turawan daga yammacin Turai da kuma uwar gijiyarsu Amurka.

Koma baya da talauci da yunwa kashe-kashen rayuka ba gaira ba dalili da sunan tawaye (Insurgence), satar mutane domin karɓar kuɗin fansa (kidnapping) kai da duk wasu hanyoyi na ta’addanci tsare-tsare na mulkin mallaka. Domin kullum ku garzaya gurinsu, don neman shawarwari da za su sake dulmiya ku cikin rijiya gaba dubu da suka haka muku.

Idan muka yi la’akari da shawarwarin da hukumomin duniya suke ba wa ƙasashe masu tasowa irin Najeriya shawari ne da suke ba wa ’yan mulkin mallaka ƙasar Birtaniya da Faransa da Jamus da Portugal da Italiya da Sifaniya (Spain) da Amurka, kuma a yanzu ƙasar China, wato Sin da Rasha da ƙasar Saudiyya da sunan tallafi ko kuma zuba jari.

Mun ji wannan tallafi (taimako) haɗin gwiwa ne tsakanin ƙasashen Musulmi (OIC) da kuma ofishin Majalissar ɗinkin Duniya mai kula da harkokin jinƙai (OCHA).

Duk wata shawara daga Bankin Duniya ko daga Hukumar Bada Lamini ta Duniya (IMF) to, ka tabbata guba ce mai hadarin gaske, idan ku ka faɗa sai ya kai ku shekaru 50 zuwa 100 ba ku fita ba. Haka shwara daga ƙungiyar kyautata ilimi da kimiyya da al’adu ta Majalisar ɗinkin Duniya (USBNCO) shawara ce daga mutanen banza, mayaudara za ka ji zance cau kamar zuma dabara ce ta mai tarkon ungulu, wanda ake cewa, ‘sai da kash’, shi ya sa ko ka ƙalubalance su ba sa mayar da martani, wadda ita ma dabara ce da ake cewa, “mai tarko ba ya ɗaga kara”.

Amma a gode wa tsohon Shugaban Hukumar Zaɓen Nijeriya, Farfesa Attahihu Jega, wanda kuma shine tsohon Shugaban Jami’ar Bayero da ke Kano da fito fili ba tare da tsoro ba, ya ba wa gwamnatin shawarwarin Bankin Duniya da ita Hukumar IMF a wata maƙala da ya gabatar ga daraktoci da suke tattaunawa kan batun samar da ingantacciyar gwamnati da za ta iya farfaɗo da tattalin arziki.

Wannan batu na Jega ya yi kyau, amma kash maciji ne ba tare da an sare kansa ba. Malaman Jami’o’i da manyan makarantun fasaha da makarantun ilimi mai zurfi su za a yi wa gyaran fuska, duk malamin shi da ɗalibansa, ba su zo da wani bincike a fannin da ya ƙware a yi masa ritaya babu fansho babu garatute bayan wasu shekaru da samun digirinsa na digirgi, wato PhD, kuma ba za a ciyar da shi gab aba-zuwa farfesa, balle ma har ya tafi yajin aiki. Idan suka tafi yajin aiki sai a dabbaƙa tsarin nan na “no work no pay” ko na wata ne.

Bayan ga haka, a samar  da hakuma ta malaman ilimin gaba da sakande “tertiary institutions” na sa kai wato ‘ɓolunteers’ su muka matasa kamar yadda muka shafada sune ginshikan, kuma turakun ci gaban al’umma kowacce iri. Da matasa ne ilimi yake habaka, yaduwa a tsakanin al’umma. Zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma yalwar arziki yake samuwa. Matasa sune ma’abutan yada duk wata akida mai kyau ko aka sin haka a cikin kasa.

Da matasa sun rungumi akidar kishin kasada yankinsu da garinsu da sana’ar gidansu komai kankantarta, sune zasu zamanantar da ita kamar yadda muke gani a sauran kasashen duniya, inda matasansu basa raina sana’a, suna garmama nag aba dasu da kuma kankantarsu basa raina sana’a suna girmama nag aba dasu da kuma kannansu. Matasa na gari basu san kyashi ba da wayar jinsi ko kabila ko darika. Basu ba fitina balle har ta kai ga matakin zubar da jinni.

Maganar gaskiya, duk al’ummar da tayi watsi da tarbiyar matasan cikin ta, basu san komai ba sai yajin ayki daga malamsu na jami’o’I sai cin hanci da rashawa, sai ingiza zanga-zanga daga kungiyar kwadago da kuma fasa da ragargaza dukiyar hakuma kamar bututun harkar danyan man fetur da katse wayo bayar da wutar lantarki.

Maganar gyaran ƙasa, magana ce ta kowa-da-kowa babba da yara, mata da maza, amma matasa su ne kan gaba daga tarbiyyar da suka samu daga dattawansu, kamar yadda ya wanzu a baya, amma ba shawara daga mutanan da suka yi mana daurin talala sun yi mana takunkumi sun turke mu gab akin kyalle sun yi mana madadi. Har abada sai lokacin da mu ka katse waɗannan tarakuna.

By ukarofi