Turmutsutsun Ibadan: Kotu ta tusa ƙeyar tsohuwar matar Oonin Ife zuwa kurkuku

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Allƙalin wata kotun Shari’a dake Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, ya umarci a tsare waɗansu mutane uku da aka alaƙanta su da hannu a iftila’in da ya auku a makarantar Bashorun Islamic High School.

Mutanen sune Frinsifal ɗin makarantar, Mista Abdullah Fasasi da mai gidan rediyon Agidigbo Alhaji Oriyomi Hamzat da kuma Naomi Silekunola, wadda ita ce tsohuwar matar Ooni na Ile Ife, Adeyeye Ogunwusi.

Alƙali Olabisi Ogunkami wanda ya yi hukunci game da lamarin ya umarci a tsare mutane ukun a gidan yarin Agodi.

Ana zargin mutanen ne bisa aikata laifuka huɗu da suka ci karo da dokar manyan laifuka ta jihar.

A makon da ya gabata ne aka samu wani iftila’i da ya auku a makarantar, a wajen wasan yara wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama inda tun daga lokacin ne ƴan sanda suka yi ram da mutane ukun.

By Babaji