
Hukumar kula da ƙwallon ƙafa ta Turai (UEFA) na shirin ƙaddamar da shari’a a ƙasar Switzerland kan shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasa-da-ƙasa (FIFA), Gianni Infantino da wasu jami’an hukumar.
Batun ya samo asali ne daga wani shirin FIFA da aka yi watsi da shi na siyar da kaso 20 na haƙƙin kasuwancin gasar cin kofin duniya da wasu gasa ga masu zuba jari masu zaman kansu kan Dala biliyan 4.2.
UEFA na zargin cewa an tsara shirin ba tare da cikakken bin tsarin gudanar da FIFA ba, kuma tana son samun wasu takardu da shaidu daga hukumomin FIFA da masu zuba jari domin amfani da su a shari’ar da ake shirin kaiwa kotunan Switzerland.
An janye shirin ne a ranar 1 ga Agusta bayan ya fuskanci kakkausar suka daga wasu manyan masu ruwa da tsaki a ƙwallon ƙafa. Lamarin na ƙara tsananta rashin jituwa tsakanin UEFA da FIFA, yayin da ake tunkarar zaɓen shugaban FIFA na gaba a shekarar 2027.
