Ummarar Sarkin Ibadan ta jawo cece-kuce kan dangantakar addini da al’adar Yarabawa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Mai martabar Sarkin ƙasar Ibadan, Oba Rashidi Adewolu Ladoja, Arusa I, ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta bayan yaɗuwar hotunansa yayin da yake gudanar da ibadar Umrah a Saudiyya.

Oba Ladoja, wanda shi ne basaraken gargajiya na 44 a tarihin ƙasar Ibadan, ya je Saudiyya ne domin gudanar da ibadar Umrah, a wani ɓangare na bukukuwan cikar shekara guda da hawansa karagar mulkin ƙasar badan a shekarar 2025.

Ladoja, wanda tsohon gwamnan Jihar Oyo ne kuma a halin yanzu yake jagorantar Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Jihar Oyo, an cauke shi hoto a Saudiyya tare da wasu mutane uku yayin da suke gudanar da ibadar. Sai dai wasu daga cikin hotunan sun haifar da muhawara, musamman saboda an ga basaraken ba ya sanye da hula ko wani abin rufe kai, yayin da yake cikin kayan Ihrami.

Wasu masu amfani da kafafen sada zumunta sun nuna mamaki kan yadda basaraken ya bayyana, inda suka ce bai kamata a ga wani basarake mai irin wannan matsayi yana tafiya cikin ibadar Umrah ba tare da rufe kansa ba. Sai dai wasu Musulmi da kuma mutanen da suka san ƙa’idojin gudanar da Umrah sun bayyana cewa namiji ba ya rufe kansa yayin da yake cikin Ihrami, kuma hakan na daga cikin dokokin ibadar. Sun ce wannan al’ada tana kuma nuna tawali’u da daidaiton dukkan bayin Allah a gabanSa, ba tare da la’akari da matsayinsu na siyasa, sarauta ko arziki ba.

Muhawarar ta ƙara haifar da kiraye-kirayen a mutunta bambancin addini da fahimtar ibadun Musulunci, inda wasu suka kuma kawo misalan wasu sarakunan gargajiya da ke shiga harkokin addini daban-daban. Wasu daga cikin masu sharhi sun ce ya kamata a fi mayar da hankali kan manufar ibadar da muhimmancinta na ruhaniya, maimakon mayar da hankali kan yadda basaraken ya bayyana a lokacin da yake cikin Ihrami.

A gefe guda, wasu masu amfani da kafafen sada zumunta sun soki ziyarar ƙasar Ibadan zuwa Makka, yayin da wasu kuma suka kare shi, suna mai cewa kowa yana da ’yancin gudanar da addininsa.

By ukarofi

Leave a Reply