Gwamnatin Tarayya ta sha alwashin ƙara ƙaimi wajen yaƙi da sikila

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayya ta sake jaddada aniyarta ta rage giɓin samun kulawa da damar rayuwa tsakanin mutanen da ke fama da cutar sikila, yayin da Nijeriya ta haɗa hannu da wasu ƙasashe da ƙungiyoyin duniya wajen ƙaddamar da sabuwar ƙawance da nufin sauya tsarin kula da masu fama da cutar.

ƙaramin Ministan Lafiya da Jin Daɗin Jama’a, Dakta Iziaƙ Adekunle Salako, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a yayin ƙaddamar da shirin “OneSCD – ƙawancen Duniya na Bunƙasa Daidaito da Sauya Tsarin Kula da Cutar Sikila”, wanda aka gudanar a Majalisar ɗinkin Duniya da ke New York, a gefen taron Babban Taron Majalisar ɗinkin Duniya karo na 81.

Nijeriya, Uganda, Indiya, Jamaica da St. Kitts and Neɓis ne suka shirya ƙawancen tare da Asusun Tallafa wa Yara na Majalisar ɗinkin Duniya (UNICEF), Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), Cibiyar Kula da Cututtuka ta Afirka (Africa CDC), Asibitin Binciken Cututtukan Yara na St. Jude da kuma ƙungiyar Duniya ta Cutar Sikila.

Da yake gabatar da jawabin maraba a madadin Nijeriya, Dakta Salako ya ce kusan mutane miliyan takwas ne ke fama da cutar sikila a faɗin duniya, inda sama da kashi 75 cikin 100 daga cikinsu ke zaune a yankin Afirka kudu da hamadar Sahara.

Ya ce, da dama daga cikin masu fama da cutar na rasa rayukansu kafin su kai shekaru biyar sakamakon matsalolin da za a iya kare su ko kuma magance su idan aka samu kulawar da ta dace.

Ministan ya bayyana Nijeriya a matsayin ƙasar da ke da mafi girman nauyin cutar sikila a duniya, inda ya ce ana haifar jarirai tsakanin 150,000 zuwa 180,000 da cutar a duk shekara.

A cewarsa, wannan ne ya sa gwamnatin Nijeriya ta sanya yaƙi da cutar cikin manyan abubuwan da ta mayar da hankali a kansu, musamman a fannonin rayuwar yara, lafiyar mata masu juna biyu, kiwon lafiya na matakin farko da kuma samar da kiwon lafiya ga kowa.

Ya ce Nijeriya na ƙarfafa matakan da take ɗauka ta hanyar wani shirin ƙasa da ke ƙarƙashin Ma’aikatar Lafiya da Jin Daɗin Jama’a ta Tarayya, Kwamitin Kula da Shirin na Ƙasa da kuma ƙa’idojin kula da gano cutar da kuma magance ta.

Dakta Salako ya bayyana cewa ana gudanar da shirye-shiryen gwajin jarirai da aka haifa domin gano cutar tun da wuri a jihohin Legas da Kano, da kuma Babban Birnin Tarayya, ta hanyar cibiyoyin haihuwa, allurar rigakafi da cibiyoyin kula da lafiya na matakin farko.

Ya ƙara da cewa an kafa cibiyoyin ƙwarewa guda shida masu dauke da na’urorin HPLC, waɗanda ake amfani da su wajen yin gwaje-gwaje na musamman don gano cutar, a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Ministan ya ce gwamnati na kuma ƙoƙarin inganta damar samun gwaje-gwajen cutar da magunguna masu sauƙin kuɗi, horas da ma’aikatan lafiya, gina hanyoyin tura marasa lafiya zuwa cibiyoyin da suka fi ƙwarewa, tare da shigar da bayanan masu fama da sikila cikin tsarin tattara bayanan kiwon lafiya na ƙasa.

Ya ce ana kuma neman hanyoyin samar da ɗorewar kuɗaɗen kula da cutar ta hanyar inshorar lafiya da haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu, domin rage nauyin kuɗin jinya da ke kan iyalai.

Dakta Salako ya ce ƙoƙarin da duniya ke yi wajen yaƙi da cutar sikila ya fuskanci matsalar rashin daidaito da kuma rashin ba cutar fifikon da ya dace, musamman ganin cewa mafi yawan masu fama da ita suna cikin ƙasashe masu ƙaramin ƙarfi da matsakaicin ƙarfi.

Ya ce, wannan ne ya sa aka kafa OneSCD, domin haɗa jagororin siyasa, ƙwararru da kuma hanyoyin samar da kuɗaɗe wajen tallafa wa matakan da kowace ƙasa ke ɗauka da kanta.

Ya ce a matsayinta na ɗaya daga cikin ƙasashen da ke jagorantar wannan shiri, Nijeriya za ta haɗa tsarin gano cutar tun da wuri da cikakkiyar kulawa a dukkan matakan kiwon lafiya, tare da ƙarfafa riƙon amana ta hanyar bayanai da samar da kuɗaɗe. Ya kuma ce gwamnati za ta sanya marasa lafiya da iyalansu a tsakiyar manufofin kula da cutar tare da raba abubuwan da ta koya da sauran ƙasashe.

Ministan ya yi kira ga abokan hulɗar ci gaba, gidauniyoyi da kamfanoni masu zaman kansu da su zuba jari wajen tsarin kiwon lafiya da ƙasashe suka mallaka da kansu, tare da faɗaɗa shirye-shiryen da aka tabbatar da tasirinsu wajen yaƙi da cutar sikila.

By ukarofi

Leave a Reply