Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
A ƙarkashin shirin samar da ci gaban ƙasa na ‘Renewed Hope Initiatiɓe RHI’ uwargidan shugaban ƙasa Oluremi Tinubu ta bada gudunmawar naira biliyan ɗaya domin ci gaba da yaƙi da tarin fuka a ƙasar nan.
Oluremi ta faɗi haka ne a taron ranar cutar tarin fuka ta duniya da aka yi a Dauka dake Abuja ranar Litini.
Wannan shine karo na biyu da Remi Tinubu ke bada gudunmawa domin yaƙar cutar a ƙasar nan.
A shekarar 2024 Tinubu ta bada gudunmawar naira biliyan ɗaya domin nuna jaruntanta a yaƙi da cutar a ƙarƙashin shirin ‘Global and National Stop TB’.
Ta ce sakamakon binciken da WHO ta gudanar ya nuna cewa mutum ɗaya na mutuwa a cikin mintuna bakwai a duniya a dalilin cutar.
“A zaman wannan taron da muke yi mutane da dama na mutuwa a ƙasar nan a dalilin cutar idan har ba mu gaggauta ɗaukan matakan kawar da cutar ba.
Oluremi ta ce za ta yi amfani da matsayinta domin daukaka muryoyin masu fama da cutar a ƙasar nan domin ganin an samar da kula ga masu fama da cutar musamman mata, yara ƙanana da waɗanda ake nuna wa wariya.
A tsokacin da ya yi wakilin WHO a Nijeriya, Walter Mulombo ya tabbatar cewa cutar za a iya kawar da shi idan har an haɗa hannu gaba ɗaya an mata wa gwamnati baya.
Mulombo ya yi kira ga gwamnati da ta zage damtse wajen ware kuɗaɗen yaƙi da cutar yana mai cewa rashin ware kuɗaɗen ka iya kawo koma baya a nasarorin da kasan ta samu shekaru 20 da suka gabata.
Ya tabbatar cewa WHO za ta ci gaba da mara wa gwamnatin Nijeriya baya domin yaƙan cutar daga ƙasar.
Tarin fuka cuta ce da ƙwayoyin cutar ‘mycobacterium tuberculosis’ ke hadassa shi a huhun mutum sannan yana cuta na biyu bayan Korona dake kisa kuma aka fi kamuwa da ita a duniya.
Sakamakon binciken da WHO ta gabatar a 2024 ya nuna cewa mutum miliyan 10.8 ne suka kamu da cutar a 2023 inda daga ciki mutum miliyan 1.6 sun mutu sannan kashi 12% daga cikin yara ne da matasa.
Nijeriya ta zama ƙasa ta shida a duniya sannan ƙasa ta farko a Nahiyar Afrika da cutar ta fi yi wa katutu a duniya.
An ware ranar 24 ga watan Maris ta kowace shekara a matsayin ranar tunawa da yaɗuwar Tarin Fuka a duniya.
A wannan rana jami’an lafiya na wayar da kan mutane game da cutar da illar dake tattare da nuna wa masu fama da cutar wariya.
Bana gwamnatin Nijeriya na da burin inganta kulan da masu fama da cutar ke samu musamman a yankin karkara.
