Wa zai auri ma’aikaciyar lafiya? (2)

Daga AMINA YUSUF ALI

Bismillahir rahmanir rahim. Da fatan masu karatu suna tare da ni kuma za su ci gaba da jimirin karanta wannan jarida tamu mai farin jini wato Manhaja. Mai fitowa kowanne mako. A makon da ya gabata ne muka kawo muku bayani masu yawa a game da yadda mata ma’aikata musamman waɗanda suke aiki a ɓangaren lafiya suke fuskantar ƙalubale da dama. Walau a wajen aikin nasu, ko gidajen iyayensu, har ma da gidajen aurensu da kuma sauran fannoni na rayuwarsu. Wasu daga cikin kalubalen da muka zano su ne; yadda mutane suke gudun su aure ko kuma a kafa musu sharaɗin su ajiye aikin nasu kafin a aure su ko kuma a ƙi ba su haɗin kan gudanar da aikin nasu bayan an aure su.

Ɗan ƙarin bayanin da zan yi shi ne: waɗannan matsalolin kusan dukkansu suna faruwa ga sauran mata masu aiki. Amma abin ya fi tsanani a ɓangaren ma’aikatan lafiyar. Kuma matsalolin dukka suna faruwa ne saboda wasu dalilai da muka fara bayarwa a wancan makon. Kuma muna sa ran za mu ci gaba a wannan makon. Dalilan da muka kawo sun haɗa:

  1. Aikin ma’aikatan lafiya aiki ne da yake cin lokacinta sosai. Don akwai lokacin da za a kwana ma a wajen aikin. Duk da dai Bahaushe musulmi yana fatan idan ya kawo matarsa ko wata ‘yaruwarsa asibiti haihuwa da daddare, yana tsananin son ya ga ma’aikaciyar lafiya mace ce za ta duba matar tasa. Amma abin tambayar ita ce; shin zai iya bari matarsa ta zama ita ce wannan ma’aikaciyar wacce za ta duba wata ‘yaruwarta macen? Wannan tambaya ce da ya kamata mu yi wa kanmu. Da mijin wannan ma’aikaciyar lafiyar ko iyayenta su ma sun killace ta sun hana ta aikin za a samu wannan rufin asirin? Don haka ashe aikinsu yana da matuƙar muhimmanci a wajen al’umma.
  2. Tana samun kuɗi sosai wataƙila ma fiye da mijin. Wannan yana daga dalilan da wasu masu ba da shawara suke ba wa mutane don kada su auri ma’aikaciyar lafiya. Wasu ma suna kan ra’ayin cewa in dai mace tana aiki tana samun kuɗi fiye da miji to ba za ta juyu a wajensa ba. Ma’ana ba za ta yi masa biyayya ba. Amma abin lura shi ne; ita biyayyar aure ta ta’allaƙa ne fa a irin tarbiyya ko rashinta ta mace. Mace mara tarbiyya ko ba ta taɓa zauna benci ba, ba za ta yi biyayya ba. Haka mace mai tarbiyya samun Duniya ba zai hana ta biyayyar aure ba. Rashin gwama matsalar rashin biyayyar da ilimi ko kuma samun kuɗin mace da rashinsu zai fi mana sauƙi.
  3. Mace mai ilimi ko wacce take aiki ba ta da kamun kai; Wannan ma da ita da matsalar da aka zana a sama dukkansu Juma ne da ɗan Jummai. Wato dukkansu hasashe ne na wasu mutane. Da aka gina shi a kan rashin masaniya kan alaƙar ilimin bokon mace da ɗabi’unta. Gaskiyar magana ita ce, ilimin boko ko zuwa aikin mace ba zai sa ta zama mara kamun kai ba. Sai dai da ma tana da halayyar rashin kamun kan. Haka idan mace mara kamun kai ce sai ta yi, ko da kuwa ba ta iya rubuta sunanta ba. Don haka don Allah a dinga yi wa ma’aikatan lafiya uzuri da kyakkyawan zato. Su ma ana samun nagari kamar yadda ake samun ɓata-gari a cikinsu.
  4. Ta fiye yawo ba ta zama: wannan yawo da take yi aikinta ne ya jawo haka. Amma kuma da wuya mace ma’aikaciya da ta san me take yi ta fice daga gidanta ba tare da ta yi dukkan ayyukanta ba ma. Har ma da girki. Wacce ba ta yi kuwa, lallai ba ta san me take yi ba. Kuma ko da za a yi bincike za a tabbatar da haka.
  5. Ba za ta iya zama a gida din-din-din kamar sauran mata ba. Wnnan kuma da ma dole a yi haƙuri a kau da kai.
  6. Danginsa da abokai ba za su amince ba: Ya kamata wanda zai aure ya sani. Ba abokinsa ko ɗanuwa ne zai zauna masa da matarsa ba shi ne zai zauna da kayarsa. Don haka wajen zaɓen abokiyar rayuwa, sai ya zaɓo wacce za ta dace da rayuwarsa ba wacce ta dace da ra’ayin wani ɗanuwansa ko abokinsa ba. In dai ba iyaye ne ko magabatansa suka yi bincike suka gano rashin dacewar auren ba, kawai ya bi ra’ayin kansa. Domin shi aure ana ƙulla shi kuma ya yi ƙarko idan masu yin sun kwanta a rayukan juna kuma akwai fahimta a tsakani. Ɗanuwa, ka toshe kunnuwanka.Ka yi abinda ya dace da rayuwarka.
  7. Ba lallai ta haifa maka yawan zuri’ar da kake buƙata ba: Mutane suna ganin mace ma’aikaciya dole takan ƙayyade iyali domin ta samu sararin yin aiki yadda ya kamata. Don haka, mazuga kan yi huɗubar kada a aure su saboda haka. Ɗanuwa, ka sani dukkan zuri’ar da Allah ya rubuta maka sai ka haife su, labudda. Haka kuma shi tsarin iyali taimako ne a gare ka. Domin lafiyar matarka da ma nutsuwarku gabaɗaya. Sannan kuma idan kana ganin matarka tana tauye maka yawan zuriyyar da za ka haifa. A matsayinka na namiji, kana da zaɓi na ƙaro wata matar idan kana da halin yin hakan. Idan ba ka da hali ku zauna ku tattauna da matarka a kan haka.
  8. Yawan shekarunta: Duk wanda ya san karatun harkar lafiya musamman na likitanci, ya san akan ɗauki lokaci mai tsaho ana yin karatun. Hakan zai sa mace shekarunta su tafi sosai. Maza da yawa a yankin arewacin kasar nan sun fi sha’awar auren mace ‘yar ƙasa da shekaru ashirin ko ashirin da kaɗan. Musamman idan auren fari ko da kuwa shi shekarun nasa sun ja sosai. Domin suna ganin idan suka auri wacce ta haura waɗancan shekarun za ta fi ƙarfinsu. Wannan kuma za a iya cewa fahimtarsu ce haka. Domin a aure tarbiyya da halayyar wacce ka aura ce take tasiri wajen yi maka biyayya ba shekarunta ba. Wani lokacin ma karamar yarinya mai rawar kai sai ta fi gwara kan namiji a kan mai shekaru. Wacce ta riga ta mallaki hankalin kanta. Don haka ba shekaru ne dafin aure ba. Kawai a samo wacce ta dace.
  9. Ba ta da lokacin tarbiyya da kula da yaranta: wannan ma duk za mu ce hasashe ne wanda aka gina bisa igiyar zato. Don ko a unguwanninmu ba za mu rasa ganin yaran da iyayensu suke wuni tare da su kullum ba .Amma yaran ba su samu kulawa da tarbiyya ba. Ashe abin ba yawan lokacin ba ne. Dagewa a tarbiyyar ne, da kuma jajircewa wajen bin yaran da addu’o’in shiriya.

Wadannan dalilaibna sama da na bayar suna daga cikin raunanan dalilan da akan bayar domin a hana auren waɗannan bayin Allah masu aikata alkhairi. Wato ma’aikatan lafiya. Ina ma a ce al’ummarmu za su kau da kai su duba alkahiran da suke samarwa a cikin al’umma su ƙarfafe su ta hanyar aurensu da kuma kyautata musu bayan auren. Domin idan aka auri mace ma’aikaciya ba wai ita kaɗai aka taimakawa ba. Kai ma mai auren za ka nasu da wasu fa’idoji kamar haka:

*Mace ma’aikaciya tana samun abin hannunta dai-dai gawargwado. Ba za ta sa maka ido a kan samunka ba. Wata ma har tallafa maka take yi. Hasali ma kusan duk wani kuɗi da ta samu kan ‘ya’yanka da gidanka yake tafiya.

*Mace ma’aikaciya ba ta da yawan ƙorafi a kan aikinka. Musammn idan yanayinka ya canza. Ko kuma idan ba ka dawo gida yadda ka saba ba da sauransu. Saboda ita ma ta san canje-canjen da yakan iya faruwa a wuraren aiki.

*Mace mai aiki takan fahimci yanayinka.

*Idan ma’aikaciyar lafiya ce, yanayin aikinta ya koya mata tausayi da juriya da haƙuri. Don haka za ta tafiyar da hakan a zamantakewar aurenku.

*Mace ma’aikaciya ko mutuwa ka yi kana da yaƙinin cewa yaran da ka haifa ba za su tagayyara ba. Tunda tana da yadda za ta tallafa wa rayuwarsu.

*Mace ma’aikaciya ta fi wacce ba ta aiki tattalin kayan abincin gida da sauran kayan amfanin gida. Saboda ita ma ta san zafi da ciwon nema.

*Ma’aikaciya ba da lokacin kanta ballantana ta samu lokacin takura maka da matsalolinta na yau da kullum. Haka kuma samar da tazara a zamantakewa yana matukar kara soyayya. Za ku dinga begen juna.

*Ma’aikaciya ba ruwanta da sa ido a kan abinda kake yi wa danginka ko iyayenka. ko kuma ta ce dole sai ka ɗauki ɗawainiyar iyayenta ko dangi. Domin ita ma tana da samunta dai-dai gwargwado.

  • Idan kana auren malamar makaranta yaranka za su taso da hazaka da ƙoƙarin ɗaukar karatu. Kuma wannan ba sabon abu ba ne. Mutum zai iya duba ga mutanen da suke kewaye da shi don tabbatar da hakan.

*Ma’aikaciya tana bukatar hutu. Kuma takan huta kamar a ƙarshen sati. Hakan yakan ba ka damar kai ma ka huta ba tare da takurawa ba.
Gogewar da take samu a yanayin aiki zai sa ta iya taimaka maka wajen samar da dabarun da za ka inganta rayuwarka da sana’arka.